Bayan Kwanaki 9 da Mutuwar Matarsa, Gwamna Ya Bude Bakinsa, Ya Fadi Halayen Marigayiya

Bayan Kwanaki 9 da Mutuwar Matarsa, Gwamna Ya Bude Bakinsa, Ya Fadi Halayen Marigayiya

  • Bayan shafe kwanaki kusan tara da mutuwar matarsa, Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya yi magana a karon farko
  • Gwamna Eno ya ce zai yi matukar kewar marigayiya Patience Umo Eno har karshen rayuwarsa saboda halayenta
  • Gwamnan ya yi godiya ga shugaba Bola Tinubu da yan jihar Akwa Ibom da sauran al'umma kan addu'o'in da suka yi mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya yi magana bayan mutuwar mai dakinsa.

Gwamna Eno ya yi martanin ne bayan kwanaki tara da mutuwar matarsa, Mrs Patience Umo Eno.

Gwamna ya yi magana game da mutuwar matarsa bayan kwanaki 9
Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya bayyana kaduwarsa bayan mutuwar matarsa. Hoto: @Ricosi89/@OfficialPDPNig.
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu bayan mutuwar matarsa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin X na PDP ya wallafa a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

'Yan APC maƙiya talaka ne,' Kwankwaso ya kawo mafita da ya illata jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya bayyana marigayiyar a matsayin mace da kowane namiji ke muradi irinta a rayuwarsa.

Eno ya ce tabbas zai yi matukar kewarta saboda irin yadda ta zamo abokiyar addu'a da garkuwa a rayuwarsa.

"Fasto Patience Umo Eno mace ce wacce kowane namiji zai so a matsayin mace ta gari."
"Tabbas zan yi kewarta har karshen rayuwata."

- Umo Eno

Gwamna Eno ya godewa Tinubu da al'umma

Gwamna Umo Eno ya yi godiya ta musamman ga hsugaba Bola Tinubu kan ta'azziyarsa gare shi saboda mutuwar matarsa.

Gwamnan ya kuma godewa yan jihar Akwa Ibom da sauran al'umma da yan siyasa kan addu'o'i da suka yi wa marigayiyar.

Tinubu ya jajantawa gwamnan Akwa Ibom

Kun ji cewa fadar shugaban kasa ta mika ta'aziyyar shugaba Bola Tinubu bisa mutuwar matar gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.

Kara karanta wannan

Bayan cire VAT a gas da dizil, gwamnati ta yi albishirin saukin farashin wutar lantarki

Patience Eno ta rasa ranta a ranar Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024 bayan rashin lafiya a wani asibiti da ke jihar, ba a fadi cutar da ta yi ajalinta ba.

Sakon ta'aziyyar na kunshe a cikin sanarwar da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin Facebook a ranar Juma'a 27 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.