"Na Ji Zafi Sosai" Buhari Ya Magantu kan Iftila'in da Ya Faru a Niger, Ya Kora Ruwan Addu'o'i
- Yayin da ake cigaba da tsamo gawarwaki ta ayyukan ceto a jihar Niger, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziya
- Buhari ya bayyana halin da ya shiga bayan samun labarin kifewar jirgin ruwa makare da mutane masu bikin Maulidi
- Tsohon shugaban ya yi addu'ar Allah ya yi wa wadanda suka rasu rahama da fito da wadanda suka bace cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan iftila'in da ya faru a jihar Niger.
Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu yayin wani mummunan hatsarin jirgin ruwa.
Buhari ya kadu da hatsarin jirgin ruwa a Niger
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Buhari ya ce ya kadu da rashin da aka yi bayan kifewar jirgin ruwan da ke makare da masu zuwa bikin Maulidi.
Buhari ya ce ya ji zafin rashin da aka yi yayin da ake cigaba da tsamo gawarwaki da ceto wasu da lamarin ya rutsa da su.
Muhammadu Buhari ya yi ta'azziya ga jihar Niger
Ya tura sakon ta'azziya ga gwamnatin Niger da kuma al'ummar jihar kan wannan abin bakin ciki da ya afku.
"Ina alhini da jajantawa iyalan wadanda suka rasu a hatsarin jirgin ruwa."
"Ina addu'ar samun nasara wurin tsamo sauran wadanda suka makale."
"Muna addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da addu'ar Allah ya tseratar da wadanda suka bace cikin kishin lafiya."
- Muhammadu Buhari
Tinubu ya kadu da hatsarin jirgin ruwa
Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da bincike domin gano dalilin yawaitar haɗurran jiragen ruwa a Najeriya.
Shugaban ƙasar ya kuma jajantawa gwamnatin jihar Neja da da sauran al'umma bisa haɗarin jirgin da ya rutsa da kusan mutum 300.
Tinubu ya umarci hukumar NIWA ta lalubo hanyoyin da ya kamata a bi domin magance haɗurran kwale-kwale a sassan kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng