1 ga Oktoba: Ƙasar Rasha Ta Maida Martani kan Zanga Zangar da Aka Yi a Najeriya

1 ga Oktoba: Ƙasar Rasha Ta Maida Martani kan Zanga Zangar da Aka Yi a Najeriya

  • Ƙasar Rasha ta maida martani kan zargin da ake mata na hannu a shirya zanga-zangar da aka yi ranar 1 ga watan Oktoba a Najeriya
  • Gwamnatin Rasha ta ce Burtaniya, Amurka da Ukraine ne ke kokarin lalata alaƙarta da kasar, amma ba ita ta kitsa zanga-zangar ba
  • Rasha ta kuma roki gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da raɗe-raɗin, inda ta ce tana mutunta kowace ƙasa mai zaman kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamnatin ƙasar Rasha ta bayyana cewa ba ta da hannu a sabuwar zanga-zangar da aka yi ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 a Najeriya.

Gwamnatin ta ce tana zargin ƙasashen yammacin duniya ne ke kulla munafurcin da zai ruguza kyakkyawar alaƙar Rasha da Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata ƙungiyar addinin Musulunci ta dura kan Shugaba Tinubu, ta faɗa masa gaskiya

Tinubu da Putin.
Kasar Rasha ta musanta hannu a zanga-zangar da aka yi ranar 1 ga watan Oktoba a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Vladimir Putin
Asali: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da gwamnatin kasar Rasha ta aikawa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yaɗa labarai na ofishin jakadancin Rasha a Najeriya, Yury Paramonov ya turawa Daily Trust wannan takarda, inda Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar.

Meyasa ake zargin ƙasar Rasha?

Idan ba ku manta ba wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa daga tutar Rasha suna rera taken ƙasar, wasu kuma na rike da alluna masu ɗauke da saƙonni.

Ana zargin Rasha da ke da karfin fada a ji a duniya da hannu a rikicin siyasar baya-bayan nan a wasu kasashen yammacin Afirka da suka hada da Mali, Burkina Faso da Nijar.

Wannan dalilin ya sa aka fara alakanta Rasha da hannu a zanga-zangar yunwar da aka sake yi a Najeriya a farkon watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

Rasha ta musanta hannu hannu a zanga-zanga

Sai dai Rasha ta yi ikirarin cewa Amurka, Burtaniya da kuma Ukraine na alakanta ta da zanga-zangar da ake yi domin lalata alakar da ke tsakaninta da Najeriya.

Bisa haka gwamnatin Rasha ta buƙaci gwamnatin Najeriya karƙashin Bola Ahmed Tinubu ta yi fatali da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ita ke kitsa komai.

"Rasha tana mutunta Najeriya a matsayin ƙasa, ba ta tsoma baki a harkokin cikin gida na ƙasashe masu zaman kansu,"

- in ji Yury.

Yury Paramonov ya kuma miƙa sakon shugaban Rasha, Vladimir Putin na taya Najeriya murnar zagayowar ranar samun ƴancin kai karo na 64, rahoton Daily Post.

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zanga a Abuja sun gamu da cikas yayin da 'yan sanda suka rika jefa masu barkonon tsohuwa.

A ranar Talata, 1 ga watan Oktoba ne matasa suka fara gudanar da zanga zangar nuna adawa da tsadar fetur, kayan abinci da na masarufi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262