Atiku Ya Yi Ta'aziyyar 'Yan Maulidi 150 da Ake Fargabar Sun Mutu a Hadarin Jirgi

Atiku Ya Yi Ta'aziyyar 'Yan Maulidi 150 da Ake Fargabar Sun Mutu a Hadarin Jirgi

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana alhini bisa rasuwar yan maulidi a jihar Neja
  • Kwale-kwale dauke da mutane kusan 300 da suka hada mata da maza ne ya kife a Mokwa a hanyarszuwa maulidi
  • Wasu mutane kimanin 150 ne ake zaton sun rasu, kuma har yanzu ana aikin tsamo sauran gawarwakin nasuu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi takaicin kifewar kwale-kwale a jihar Neja wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka.

Mutane 150 ake fargabar sun rasa rayuwarsu yayin da kwale-kwale mai dauke da mutane 300 ya kife a jihar Neja.

Kara karanta wannan

"Na ji zafi sosai" Buhari ya magantu kan iftila'in da ya faru a Niger, ya kora ruwan addu'o'i

Niger
Atiku Abubakar ya yi ta'aziyyar rasuwar yan maulidi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce lamarin da ya afku cikin dare ya dagula aikin ceton da aka yi ya tsamo mutanen cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya yi ta'aziyyar yan maulidi

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana alhininsa ga gwamnatin jihar Neja da mazauna jihar kan rasuwar yan maulidin.

Ya yi addu'ar Allah ya ba iyalan mamatan hakuri tare da addu'ar rahama gare su, yayin da ya yi fatan samun sauki ga marasa lafiya da ke karbar magani a halin yanzu.

Atiku ya yabi masu aikin ceto

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yaba wa wadanda su ka yi aikin ceto wadanda kwale-kwalensu ya kife a yankin Mokwo da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

Ya ce duk da lamarin ya afku da daddare, amma masu aikin ceton sun sadaukar da rayuwarsu wajen zakulo wadanda su ka fada cikin ruwan.

Borno: Atiku ya yi ta'aziyyar ambaliya

A baya mun wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ka ziyarar jaje Maiduguri bayan ambaliya da ta daidaita mazauna yankin.

Yayin ziyarar, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 domin a tallafa wa wadanda su ka rasa muhallansu, suka shiga mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.