"Abin Ya Fara Yawa": Haɗarin Jirgin Ƴan Maulidi Ya Jawo Hankalin Shugaba Tinubu
- Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da bincike domin gano dalilin yawaitar haɗurran jiragen ruwa a Najeriya
- Shugaban ƙasar ya kuma jajantawa gwamnatin jihar Neja da sauran al'umma bisa haɗarin jirgin da ya rutsa da kusan mutum 300
- Tinubu ya umarci hukumar NIWA ta lalubo hanyoyin da ya kamata a bi domin magance haɗurran kwale-kwale a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan haɗurran jiragen ruwa da ke yawan aukuwa a jihar Neja.
Jihar Neja da ke Arewa ta tsakiya ta sha fama da haɗurran kwale-kwale a lokuta da dama a cikin shekara guda da ta gabata.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, ranar Talata da ta gabata da daddare aka samu wani hadarin jirgin ruwa, inda zuwa yanzu mutum 60 suka rasa rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya aika saƙon jajen haɗarin kwale-kwale
Ana zargin kwale-kwalen wanda aka ƙera da katako mai girman ɗaukar fasinjoji 100, ya dauko ƴan Maulidi kusan 300 a lokacin da ya kife a karamar hukumar Mokwa.
Kwanaki biyu da faruwar lamarin, shugaba Tinubu ya jajanta wa wadanda haɗarin jirgin ruwan ya rutsa da su da kuma gwamnatin jihar Neja.
Shugaban ƙasar ya umarci hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) ta binciki yawaitar hadurran kwale-kwale a jihar Neja da ma kasar baki daya.
Bola Tinubu ya kuma bai wa hukumar umarnin lalubo hanyoyin da za a bi domin magance haɗurran da ke yawan faruwa a ruwa a cewar rahoton Vanguard.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin bincike
Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
"Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka mutu. Ya umarci hukumar NIWA ta gudanar da bincike kan yawaitar haɗurran kwale-kwale a Neja da sauran jihohi.
“Tinubu ya kuma umurci NIWA ta fadada aikin sa ido don tabbatar da lafiyar mutane da kuma gurfanar da masu kwale-kwalen da suka karya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa da daddare.
- Bayo Onanuga.
Gwamna Bago ya kaɗu da kifewar jirgin ƴan Maulidi
A wani rahoton kuma gwamnan Neja ya nuna kaɗuwarsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane.
Mai girma Umaru Bago ya bayyana hatsarin a matsayin babban abin takaici wanda ke cike da baƙin cikin rasa rayuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng