Gwamna Zulum Ya Zagaya, Ya Gano Wadanda Suka Taimaka wajen Jawo Ambaliya
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci wasu wuraren da ambaliya ta yi gagarumar barna a jihar Borno
- Mai girma Gwamnan ya yi takaicin yadda wasu su ka gina gidaje a gabar ruwa, wanda ke hana ruwa bin hanyarsa
- Farfesa Zulum ya yi umarnin haramta gine-gine a bakin ruwa a Borno domin rage illar iftila'in ambaliya a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya fusata da mutanen da su ka gina muhallansu a gabar ruwa a jihar Borno.
Gwamna Babagana Zulum ya dora alhakin karuwar matsalar ambaliya da aka samu a baya-bayan nan kan irin wadannan gidaje.
A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi takaicin yadda gidajen bakin ruwa su ka tare hanyar da ruwan zai wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an samu gagarumar asara yayin ambaliyar, kuma irin wadannan gidaje ne su ka dagula lamarin ta hanyar hana ruwa gudu.
Gwamna ya yi takaicin ambaliya a Borno
Jaridar The Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Babagana Zulum ya ziyarci wasu wuraren da ambaliya ya masu ta'adi sosai a ambaliyar da ta gabata.
Farfesa Zulum ya yi takaicin yadda ambaliya ta lalata hanyoyi, gadar saman Gwange, makarantu da wani asibitin haihuwa da ke Gwange.
Ambaliya: Gwamna ya hana gini a hanyar ruwa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya haramta gina gidaje a gaba da kan hanyoyin ruwa a fadin jihar domin rage illar ambaliya.
Zulum ya ce za a kafa kwamiti da zai duba yadda aka yi gine-gine a hanyar ruwa da ba gwamnatin tarayya shawara kan lamarin.
Gwamna Zulum ya raba kayan ambaliya
A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya raba kayan tallafi ga mutanen da iftila'in ambaliya ya rutsa da su a Maiduguri.
Yayin kaddamar da tallafin, gwamna Babagana Zulum ya godewa gwamnatin tarayya da duk wadanda su ka tallafa da kudi da abinci domin taimakon jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng