Bayan Cire VAT a Gas da Dizil, Gwamnati Ta Yi Albishirin Saukin Farashin Wutar Lantarki

Bayan Cire VAT a Gas da Dizil, Gwamnati Ta Yi Albishirin Saukin Farashin Wutar Lantarki

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana wasu manyan ayyuka da za su inganta wutar lantarki a Najeriya
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, inda ya ce shirin zai kawo karuwar hasken lantarki
  • Adelabu ya ce ana sa ran haka zai taimaka wajen rage kudin hasken wuta da jama'ar kasar nan ke biya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce nan gaba kadan yan kasar nan za su samu saukin farashin wutar lantarki.

Ministan tarayyar ya ce za a samu rangwamen farashi ne saboda wasu muhimman ayyuka da ake yi wajen inganta samar da lantarki.

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

Adelabu
Gwamnati ta ce akwai yiwuwar rage farashin wutar lantarki Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Twitter

Trust TV ta wallafa cewa mashawarci na musamman ga Ministan makamashi, Bolaji Tunji ne ya bayyana matakin ta cikin sanarwar da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnati na bakin kokarinta wajen inganta rayuwar jama'a ta fuskar inganta rarraba hasken lantarki a fadin kasar nan.

"Ana samun saukin farashin lantarki" - Minista

Jaridar Vanguard ta tattaro Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce akalla 40% na masu amfani da wutar lantarki na samun hasken wutar yadda ya dace.

Mista Adelabu ya bayyana cewa idan aka kwatanta da kasashen Mali, Togo da Jamhuriyyar Nijar, ana shan wuta da sauki a Najeriya.

Dalilin ganin tsadar farashin lantarki

Adebayo Adelabu ya ce rashin abin hannu a wajen yan Najeriya ne ya sa ake ganin farashin wutar lantarki ya yi tsada.

Ministan makamashin ya ce amma nan gaba kadan za a samu karuwar rarraba lantarkin da yiwuwar raguwar farashin da yan kasa ke biya.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Akwai barazanar kara farashin lantarki

A wani labarin a baya kun ji cewa akwai barazanar kara farashin kudin wutar lantarki ga yan kasar nan da ke kan tsarin band A da B.

A watan Satumba 2024, gwamnati ta biya Naira biliyan 180 a matsayin tallafin kudin lantarki, wanda ya karu a kan biliyoyin da gwamnatin ta biya a watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.