Gwamna Zai Bankado Ma'aikatan Bogi, An Kafawa Ma'aikata Sharadin Karbar Albashi
- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya lashi takobin kakkabe dukkanin ma'aikatan da aka dauka ba bisa ka'ida ba a jihar
- A cikin wata sanarwar da babban sakatarensa kan watsa labarai ya fitar, Fintiri ya umarci ma'aikata su gabatar da satifiket dinsu
- Gwamnan ya ce dukkanin ma'aikacin da ya gaza gabatar da wannan takarda ba zai samu albashinsa na Oktoba da mai bin bayansa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya dauki babban mataki na tsaftace aikin gwamnati a jiharsa tare da gano ma'aikatan bogi.
An rahoto cewa Gwamna Fintiri ya umarci dukkanin ma'aikatan jihar Adamawa da su gabatar da satifiket dinsu kafin karshen watan Oktoba.
Humwashi Wonosikou, babban sakataren watsa labarai (CPS) na gwamnan jihar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafawa ma'aikatan gwamnatin Adamawa sharadi
Babban sakataren watsa labaran ya ce duk maaikacin da ya gaza gabatar da satifiket dinsa to zai rasa albashin watan Oktoba.
Humwashi Wonosikou ya ce gwamnan ya dauki matakin ne domin dakile wadanda ba su cancanta da rike mukaman gwamnati.
A cewar Humwashi:
"Gwamna Fintiri ya ba dukkanin ma'aikatan gwamnati a ma'aikatu, hukumomi da sassan gwamnati umarnin da su gabatar da satifiket dinsu."
Adamawa: Za a dakile ma'aikatan bogi
The Punch ta rahoto sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnan jihar bai ba da umarnin domin yi wa wani bi-ta-da-kulli ba, sai dai don tsaftace aikin gwamnati a jihar.
"Babu wanda zai rasa albashinsa idan har ya gabatar da satifiket dinsu kafin zuwa karshen Oktoba."
- A cewar babban sakataren watsa labaran.
Ya kuma kara da cewa yanzu ne ya dace a dauki mataki na kakkabe wadanda suka saba ka'idar daukar aikin gwamnati da kuma ma'aikatan bogi.
Fintiri ya fara biyan albashin N70,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya fara biyan ma'aikatan jiharsa sabon mafi karancin albashi na N70,000.
A ranar 19 ga watan Agusta, Gwamna Fintiri ya yi alƙawarin cewa ma'aikatan jiha za su fara cin moriyar mafi ƙarancin albashi a ƙarshen watan Agusta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng