Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Harbe Shi har Lahira a Jihar Arewa
- Wasu ƴan bindiga sun kashe shugaban APC na ƙaramar hukumar Suru a jihar Kebbi, Alhaji Bako Bala a ranar Laraba
- Hadimin gwamnan jihar, Zaidu Kofar Sabuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce maharan sun rutsa jigon APC a gonarsa
- Haka kan kuma an samu labari ƴan bindiga sun sace mutum ɗaya a yankin ƙaramar hukumar Bunza, sun harbi wani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Ƴan bindiga sun hallaka shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Suru a jihar Kebbi, Alhaji Bako Bala.
Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun sace Alhaji Baƙo Bala ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2024, kana daga bisani suka kashe shi.
Mai ba gwamnan Kebbi shawara kan harkokin talabijin da rediyo, Alhaji Zaidu Bala Kofa Sabuwa shi ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda miyagun suka kashe shugaban APC
Ya ce ƴan bindiga sun farmaki Baƙo Bala a gonarsa da ke mahaifarsa, kana suka harbe shi sannan suka tafi suka barshi cikin jini.
An garzaya da Alhaji Bako Bala zuwa asibitin FMC da ke Birnin Kebbi, inda aka yi rashin sa’a ya rasu a ranar Laraba sakamakon harbin da maharan suka yi masa.
...Ƴan bindiga sun harbi matashi a Kebbi
A wani lamari makamancin haka, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum a kauyen Matseri da ke karkashin karamar hukumar Bunza a jihar Kebbi.
Rahotanni sun nuna maharan sun kuma harbi wani matashi a harin, wanda yanzu haka yana kwance a asibitin FMC ana masa magani.
Ba a iya jin bakin Ƴan sanda ba
Duk wani ƙokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, kan kisan shugaban APC da harin sace mutumin ya ci tura.
Jihar Kebbi dai ta sha fama da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a 'yan kwanakin nan, duk da kokarin da jami'an tsaro ke yi na magance lamarin.
Ƴan sanda sun kama miyagu a Abuja
A wani labarin kuma rundunar yan sanda ta bayyana kama wasu hatsabiban yan ta'adda da su ka addabi Abuja da wasu jihohin Arewa.
Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar ta reshen birnin Abuja, SP Josephine Adeh ta ce an kama mutane hudu a maboyarsu da ke birnin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng