Wasan Buya Ya Zo Karshe, Kotu Ta Yi Sammacin Yahaya Bello kan Zargin N110bn

Wasan Buya Ya Zo Karshe, Kotu Ta Yi Sammacin Yahaya Bello kan Zargin N110bn

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja ta bayar da sammacin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello
  • Hukumar EFCC na zargin tsohon gwamnan da wawashe biliyoyin kudin al'ummar Kogi a lokacin ya na gwamnan jihar
  • Mai Shari’a Maryanne Anenih ta umarci Yahaya Bello ya bayyana a gabanta ranar 24 Oktoba, 2024 domin fuskantar shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama ta bayar da sammacin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

A umarnin sammancin da ta bayar ranar Alhamis, Mai Shari’a Maryanne Anenih ta umarci Yahaya Bello ya bayyana a gabanta ranar 24 Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Yahaya
Kotu ta bayar da sammacin Yahaya Bello Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa ana tuhumar tsohon gwamna Yahaya Bello da wasu laifuffuka 16 da su ka hada da tatike lalitar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC na tuhumar Yahaya Bello da almundaha

Hukumar yaki da yi wa kasa ta’annati (EFCC) ce ta fara shigar da kara ta na tuhumar tsohon gwamna Yahaya Bello da almundahana.

Ana zarginsa da wawashe kudin gwamnati da yawansu ya kai N110,446,470,089, wanda ya saba da sashe na 96 da 311 na kundin final kod.

Kotu ta ba da umarni kan Yahaya Bello

Kotun tarayyar ta ba hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta buga sammacin tsohon gwamna Yahaya Bello a babbar jaridar a kasar nan.

Ta kuma umarci EFCC ta manna sammancin a gidan da aka hango Yahaya Bello na karshe da wasu wurare tare da sa wani a farfajiyar kotun.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

An roki Tinubu kan shari'ar EFCC da Yahaya Bello

A wani labarin kun ji cewa sarakunan gargajiya a jihar Kogi sun roki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan dambarwar da ke tsakanin tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello da EFCC.

Sun bayyana cewa akwai barazana babba ga rayuwar tsohon gwamnan, yayin da EFCC ke zarginsa da yi wa tattalin arzikin jihar Kogi illa ta hanyar kwashe kudin jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.