Wata Ƙungiyar Addinin Musulunci Ta Dura kan Shugaba Tinubu, Ta Faɗa Masa Gaskiya

Wata Ƙungiyar Addinin Musulunci Ta Dura kan Shugaba Tinubu, Ta Faɗa Masa Gaskiya

  • Wata ƙungiyar Musulunci a Najeriya ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nemo hanyoyin yaye wahalar da ƴan Najeriya ke ciki
  • Kungiyar mai suna Hijrah ta ce babu abin da mutane ke buƙata da ya wuce samun sassauci daga matsin tattalin arzikin da suka shiga
  • Ta kuma buƙaci gwamnati a kowane mataki ta maida hankali wajen bullo da tsare-tsaren da za su kawo sassauci a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wata ƙungiyar addinin Musulunci a Najeriya 'Hijrah' ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinub] ya ɓullo da hanyoyin warware wahalhalun da ake ciki.

Ƙungiyar ta roƙi shugaban ƙasa ya fito da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki waɗanda za su share hawayen ƴan Najeriya game da kuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Garambawul: An bukaci Tinubu ya nada El Rufai da wasu mutum 4 ministoci

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Wata kungiyar addinin Musulunci ta buƙaci Tinubu ya lalubo hanyar saukakawa ƴan Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na kunshe a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na kasa, Farfesa Badmas Yusuf da sakatare, Abubakar Ayinla, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hijrah ta faɗawa gwamnati mafita

A sanarwar da ƙungiyar ta fitar ranar Laraba, ta roki kowane mataki na gwamnati ya ba da fifiko wajen inganta walwalar talakawa da share masu hawaye.

Hijrah ta kuma roƙi Tinubu ya lalubo hanyoyin magance matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta yayin da ake murnar cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.

Kungiyar ta shawarci Tinubu da cewa ya kamata, "kyautar da zai yi wa ƴan Najeriya na cika shekaru 64 da samun 'yancin kai ta zama sassauci daga halin matsin da ake ciki."

Kungiyar Musulunci ta yiwa ciyamomi nasiha

A bangaren gida kuwa, Hijrah ta yi kira ga sabbin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka rantsar a Kwara da su mulki jama'a da tsoron Allah.

Kara karanta wannan

Murnar 'yancin kai: Muhimman abubuwan da za a tuna da su daga jawabin Tinubu

Ta kuma tunatar da ciyamomi cewa gwamnatin ƙanann hukumomi na da matuƙar muhimmanci wajen samar da sauƙi da ci gaban al'umma, rahoton Leadership.

Sanata Ndume ya ba Tinubu shawara

A wani rahoton kuma Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauko hayar sojojin da za su kakkabe yan ta'adda a Najeriya.

Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan kasar nan ya ce sojojin haya na da manyan makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262