‘Za a Samu Sauki,’: Tinubu Ya Zaftare Haraji domin Saukakawa Talaka

‘Za a Samu Sauki,’: Tinubu Ya Zaftare Haraji domin Saukakawa Talaka

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cire harajin VAT a wasu kayayyaki domin kawo saukin rayuwa ga talakawa a Najeriya
  • Daraktan yada labaran ma'aikatar kudi ne ya fitar da sanarwar tare da cewa hakan na cikin kokarin gwamnatin Bola Tinubu
  • Hakan na zuwa ne bayan yan Najeriya suna cigaba da kuka kan matsalolin tattalin arziki da al'umma ke fama da su a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta zaftare haraji kan wasu abubuwa domin kawo saukin rayuwa ga talakawan kasa.

Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ce hakan na cikin matakan da take dauka domin kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya cire harajin wasu kayayyaki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin kayyakkin da aka cirewa harajin VAT akwai iskar gas da ake amfani da shi wajen girki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bola Tinubu ta zaftare haraji

A ranar Laraba ministan kudi, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnati ga cire harajin VAT a kan wasu kayayyaki.

Wale Edun ya bayyana cewa hakan na cikin tsarin saukaka haraji a kan harkokin iskar gas da mai na shekarar 2024.

Kayan da Tinubu ya zartarewa haraji

Ma'aikatar kudi ta bayyana cewa iskar gas da ake girki da abubuwan hawa ƙirar CNG na cikin abubuwan da aka cirewa harajin VAT.

Haka zalika ma'aikatar ta bayyana cewa man dizil, kayan girki, abubuwan gas na LPG, LNG da motoci masu aiki da lantarki an cire musu harajin.

Dalilin zaftare haraji a Najeriya

Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce ɗaukar matakin na cikin shirin shugaba Tinubu na kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Yadda aka kashe jagororin yan ta'adda 300 a Najeriya

Ana sa ran cewa hakan zai kara farfaɗo da sana'o'i da bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta ɓangarori daban-daban.

Shugaba Tinubu ya tafi hutu a London

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutu kasar Birtaniya a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun nuna shugaban kasar zai tafi hutun ne na tsawon mako biyu domin samun lokaci ya yi nazari kan tsare tsarensa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng