'Ko Shekaru 100 Aka ba Tinubu Bai San Yadda Zai Yi da Najeriya ba'

'Ko Shekaru 100 Aka ba Tinubu Bai San Yadda Zai Yi da Najeriya ba'

  • Fitaccen lauya, Franklyne Ogbunwezeh ya caccaki tsarin shugabancin Bola Tinubu duba da halin da ake ciki a yau
  • Ogbunwezeh ya soki Tinubu kan cire tallafin mai ba tare da samar da tsari da zai ragewa al'umma radadin kafin hakan ba
  • Ya ce kwata-kwata Tinubu bai da kwarewa na jagorantar Najeriya ko da kuwa an ba shi tsawon shekaru 100 yana mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wani lauya dan Najeriya ya koka kan yadda Bola Tinubu ke mulkar kasar ba yadda ya dace ba.

Lauyan da ke kasar Jamus, Franklyne Ogbunwezeh ya ce Bola Tinubu bai da kwarewar iya mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

An caccaki tsare-tsaren Tinubu a Najeriya
Fitaccen lauya ya koka kan rashin kwarewar Bola Tinubu a shuagabancin Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Lauya ya soki tsarin shugabancin Tinubu

Lauyan ya fadi haka ne yayin wata hira ta musamman wanda jaridar TheCable ta bibiya a karshen makon da ya gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogbunwezeh ya ce kwata-kwata Tinubu bai nemo hanyar kawo sauyi a kasar ba duba da yadda yake jagorantar ƙasar.

Ya koka kan tsare-tsaren Tinubu musamman duba da rugujewar darajar Naira da tashin farashin kaya, Sahara Reporters ta ruwaito.

"Tinubu ba shi da kwarewar jagorantar Najeriya, ko da kuwa za a ba shi shekaru 100 bai san ya zai yi ba."

- Franklyne Ogbunwezeh

Lauya ya kalubalanci Tinubu kan jagorancinsa

Ogbunwezeh ya kalubalanci Bola Tinubu ya nuna tsari daya mai kyau da ya kawo domin dakile tashin farashin kaya da daga darajar Naira.

Lauyan ya caccaki Tinubu bayan cire tallafin mai inda ya ce bai shirya komai kafin aiwatar da hakan ba wanda ya yi sanadin jefa al'umma cikin halin matsi.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan tunawa 3 da suka faru a ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai

An ba yan Najeriya hakuri kan mulkin Tinubu

Kun ji cewa yayin da ake ta yada jita-jitar cewa Bola Tinubu zai yi garambawul a mukaman Ministoci, jigon APC ya yi magana.

Barista Daniel Bwala ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri su bar Tinubu ya yi abin da ya dace a lokacin da yake so.

Bwala ya ce kafofin sadarwa ne suka kirkiri labarin kuma sun samu abin da suke so na tsawon kwanaki kan rahoton.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.