Rundunar Tsaro Ta Fadi Laifuffuka 3 da Suka Yi Sanadiyyar Korar Seaman Abbas a Soja

Rundunar Tsaro Ta Fadi Laifuffuka 3 da Suka Yi Sanadiyyar Korar Seaman Abbas a Soja

  • Rundunar tsaron kasar nan ta fito da laifuffukan da su ka sanya ta korar sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna daga aiki
  • Matar Seaman Abbas, Hussaina Iliya ce ta fara kokawa a wani shiri, take cewa an tsare mijinta na tsawon shekaru shida
  • A bayanin rundunar tsaron kasar nan, Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce sai da aka kai Seaman Abbas gabanin korarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Bayan samun labarin korar sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna daga aiki, rundunar tsaron kasar nan ta bayyyana dalilan daukar matakin.

Rundunar tsaron ta wata kotun sojoji ta samu Seaman Abbas da wasu laifuffuka uku da suka sa dole a sallame shi daga bakin aiki.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Seaman
Rundunar tsaro ta fadi dalilin korar Seaman Abbas Hoto: Brekete Family
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa kakakin rundunar tsaron kasar nan, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya tabbatar da cewa an samu Seaman Abbas da karya doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laifuffuka 3 da Seaman Abbbas ya aikata

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an kori Seaman Abbas Haruna Abbas daga aiki saboda rashin biyayya ga na gaba da shi.

Har ila yau, an samu tsohon sojan da laifin rashin da'a da aka je gaban kotunsu.

Kakakin rundunar tsaron, Janar Tukur Gusau ya ce an nemi sojan ruwan ya bayar da makaminsa, amma ya hana har ta kai ga harba harsashi 16.

An yi wa Seaman Abbas Shari'a

Rundunar tsaron kasar nan ta bayyana cewa an yi wa Seaman Abbas hukuncin kora ne bayan an bi dukkanin ka'idojin shari'a na rundunar.

Rundunar ta bayyana cewa da farko, sojan ya nuna alamun ba shi da lafiya, kuma an duba lafiyarsa a asibiti gabanin yanke masa hukuncin korar da aka yi a watan Fabarairu 2023.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Rundunar soja ta kori Seaman Abbas

A wani labarin, kun ji cewa rundunar tsaron kasar nan ta sallami Seaman Abbas daga bakin aiki bayan shafe shekaru shida a tsare, wacce matarsa Hussaina Iliya ta ce an yi ba bisa ka'ida ba.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu dai Seaman Abbas, wanda tuni ya zama farar hula ya fara samun lafiya bayan an fara duba lafiyarsa a asibiti, kuma matarsa ta nuna godiyarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.