Zanga Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyyar PDP, an Samu Bayanai
- An samu ɓarkewar wata zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar PDP ta Rivers da ke a birnin Port-Harcourt watau babban birnin jihar
- Zanga-zangar ta ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoban 2024 ta ɓarke ne domin nuna adawa da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi
- Masu zanga-zangar sun yi kira ga hukumar zaɓen jihar RSIEC da Gwamna Siminalayi Fubara su bi umarnin kotu kan zaɓen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Zanga-zanga ta ɓarke a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke birnin Port-Harcourt babban birnin jihar Rivers.
Zanga-zangar da ta ɓarke a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoban 2024 ana yin ta ne kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Tashar Channels tv ta rahoto cewa an jibge jami'an tsaro a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ake zanga-zanga a ofishin PDP?
Masu zanga-zangar dai sun yi dafifi a sakatariyar jam'iyyar PDP ne domin nuna adawarsu da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a jihar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, yawan masu zanga-zangar ya haifar da cunkoso a kan hanyar, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan jama’a.
Daga baya an ga masu zanga-zangar ɗauke da alluna da tutoci, suna rera waƙoƙin nuna adawarsu da kuma yin guje-guje a kan babbar hanyar.
Ɗaya daga cikin tutocin na ɗauke da rubutu mai cewa:
"Mutanen TAI sun ce ba su son rashin bin doka. Ba mu son a yi zaɓen ƙananan hukumomi. Dole ne hukumar RSIEC ta bi umarnin kotu, dole ne Gwamna Simi ya bi umarnin kotu."
Gwamna Fubara ya ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ayyana ranakun Alhamis da Juma'a, 3 da 4 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranakun hutu.
Gwamna Fubara ya ba da hutun kwanaki biyun ne domin bai wa ma'aikata damar komawa yankunansu domin kaɗa kuri'a a zaɓen kananan hukumomin da za a yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng