Gwamnan Arewa Ya Fitar da N11bn daga Asusun Gwamnati, Ya Sayi Jami'a a Najeriya

Gwamnan Arewa Ya Fitar da N11bn daga Asusun Gwamnati, Ya Sayi Jami'a a Najeriya

  • Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da sayen Jami'ar Khadija kan kudi Naira biliyan 11 domin inganta harkar ilimi
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa Namadi ya ce an amince da sayen jami'ar a zaman majalisar zartaswa karƙashin gwamna
  • Majalisar SEC ta kuma amince da fitar da wasu kuɗi domin ayyukan samar da ruwa, shirin WASH da sayen kayan girbi na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Majalisar zartaswan jihar Jigawa ta amince da sayen wata jami'a mai zaman kanta mai suna Jami'ar Khadija da ke garin Majia.

Majalisar ta amince da sayen jami'ar ne a wani ɓangare na manufofi 12 na Gwamna Umar Namadi wanda ya ƙunshi bunƙasa harkokin ilimi a Jigawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da hutu a ranakun Alhamis da Juma'a a jiharsa, bayanai sun fito

Gwamna Umar Namadi.
Gwamnatin jihar Jigawa ta sayi jami'ar Khadija kan kudi N11bn Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an amince da fitar da kuɗin sayen jami'ar ne a kan N11bn a wani taron majalisar zartaswan jiha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron majalisar ta SEC ya gudana ne ƙarƙashin Gwamna Umar Namadi a garin Dutse.

Yadda gwamnatin Jigawa za ta biya kudin jami'ar

Kwamishinan yaɗa labarai, harkokin matasa, wasanni da al'adu, Sagir Musa Ahmad ne ya sanar da haka ga manema labarai bayan fitowa daga taron.

Ya ce sayen jami'ar da gwammatin ta yi zai ƙara buɗe hanyoyin neman ilimi da samar da ingantaccen ilimi a Jigawa, Premium Times ta rahoto.

A cewarsa, gwamnati za ta fara biyan kashi 40% na kudin sayen jami'ar watau Naira biliyan 4.07, sannan za ta biya ragowar kashi 60% lokuta biyu nan gaba.

Gwamna Namadi ya fara aikin samar da ruwa

Bayan haka gwamnatin Jigawa ta amince da fitar da N411.8m domin ayyukan samar da ruwa a mazaɓu 23 da N400m a tsarin WASH da N1.25bn don sayen injinan girbi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar 'yan sandan da suka rasu, ya tuna da iyalansu

Ayyukan ruwan za su samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummomin karkara, yayin da injinina girbi za su tallafawa manoman jihar Jigawa.

"Gwamnatin Umar Namadi ta himmatu wajen inganta rayuwar al'ummar jihar Jigawa," in ji Sagir Musa Ahmad.

Ambaliya: Gwamna Namadi ya tallafawa mutane

A wani rahoton na daban gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya waiwayi mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a daminar nan.

Gwamnan ya amince a fitar da N315.5m domin rabawa ga mutane 15,775 da ke a sansanonin ƴan gudun hijira a inda lamarin ya shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262