‘Ya Yaudari Buhari,’ An Tono Zargin Yadda Emefiele Ya yi Gaban Kansa kan Canza Kudi

‘Ya Yaudari Buhari,’ An Tono Zargin Yadda Emefiele Ya yi Gaban Kansa kan Canza Kudi

  • Hukumar EFCC na cigaba da gabatar da shaidu a gaban kotu kan shari'ar tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele
  • EFCC ta gabatar da tsohon mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi domin yin shaida a gaban kotun tarayya
  • Shonubi ya yi zargin cewa Godwin Emefiele bai bi tsarin da shugaba Muhammadu Buhari ya umarce shi ba wajen canza kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ana cigaba da gudanar da shari'ar tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan canza takardun kudi a 2022.

Hukumar EFCC ta gabatar da tsohon mukaddashin gwamnan CBN Folashodun Shonubi a matsayin shaida a gaban kotu.

Emefiele Buhari
An samu bayanai kan canza kudi a mulkin Buhari. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa Folashodun Shonubi ya ce siyasa ta shiga harkar canza manyan kudi da aka yi a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan CBN ya zargi Emefiele da yaudarar Buhari

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi ya yi zargin cewa an yaudari shugaba Muhammadu Buhari yayin canza kudi da aka yi a shekarar 2022.

Shonubi ya yi zargin cewa kudin da aka canza ya saba yadda tsohon shugaban kasa ya umarci a yi.

Shugaba Buhari ya umarci a canza kuɗi?

Yayin da aka tambayi Shonubi ko Muhammad Buhari ya san da canza kudi, sai ya ce lallai an nuna musu takarda kan hakan.

Sai dai ya kara da zargin cewa cewa duk wata tattaunawa kan lamarin ana yi ne tsakanin Buhari da Emefiele ba tare da sun san me ake ciki ba.

Shonubi: 'Ba shawararmu kan canza kudi'

Shonubi ya kara iƙirarin cewa takardar da aka turawa shugaban kasa kan canza kudin ma Emefiele ne ya rubuta ba tare da sa hannunsu ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamna a Arewa kan tuhumar 'sace' N27bn

Tribune ta wallafa cewa bayan sauraron shaidar Shonubi, alkalin kotun ta daga sauraron shari'ar har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba.

Godwin Emefiele ya bukaci zuwa asibiti

A wani rahton, kun ji cewa Godwin Emefiele ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba shi izinin zuwa ganin likita a ƙasar waje.

Tsohon gwamnan bankin CBN ya shigar da wannan buƙata ne ta hannun lauyansa, Mathew Burkaa kuma har yanzu EFCC ba ta ce komai ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng