Ma'aikatan Jinya Na Shirin Jefa Mutanen Kano cikin Matsala, Sun Ba Gwamna Wa'adi

Ma'aikatan Jinya Na Shirin Jefa Mutanen Kano cikin Matsala, Sun Ba Gwamna Wa'adi

  • Ma'aikatan jinya a Kano sun yi barazanar shiga yajin aiki, sun bai wa gwamnatin jihar wa'adin kwanaki 15 ta biya masu bukatunsu
  • A wata wasiƙa da suka aika ofishin shugaban ma'aikatan gwamnati, sun koka kan gazawar gwamnatin wajen biyan buƙatunsu tun 2023
  • Daga cikin bukatun ma'aikatan sun haɗa da batun biyan alawus-alawus da ƙarin albashin CONHENSS ko kuwa su daina zuwa aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) reshen Kano, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 15 ta biya musu bukatunsu.

Ma'aikatan sun bayyana cewa za su tsunduma yajin aiki bayan wa'adin ya cika matuƙar gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta gaza biyan buƙatun.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Abin da ke faruwa a Kano bayan fara zanga zanga a wasu sassan Najeriya

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ma'aikatan jinya sun yi barazana shiga yajin aiki, sun ba gwamnatin Kano wa'adin kwanaki 15 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ma'aikatan jinyar sun sanar da haka ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun kakakin ƙungiyar NANNM, Kwamared Ahmad Hazmat Sharada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Ma'aikatan jinya na shirin yajin aiki

Sun ce sun zabi ɗaukar wannan matakin biyo bayan gazawar gwamnati na warware kokensu tun watan Disamba, 2023.

Ƙungiyar ta aika wasiƙar gargaɗi ga shugaban ma'aikatan jihar Kano, inda ta yi barazanar cewa ma'aikatan jinya da ungonzoma za su daina zuwa aiki idan ba a waiwaye su.

Wasu daga cikin buƙatun ma'aikatan a Kano

Wasu daga cikin buƙatun da aka zayyana a cikin wasiƙar sun haɗa da biyan kudin alawus ga ma’aikatan jinya, wanda suka nemi a ba su a ranar 2 ga Fabrairu, 2024. 

Sun kuma bukaci a biya ƙarin kaso 25% na tsarin albashi na CONHESS da dai wasu bukatu da aka zayyana a cikin wata takardar tunatarwa da aka aika wa gwamnati ranar 20 ga Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

"PDP ce sila," APC ta bayyana muhimmin aikin da ya cinye shekarun mulkin Buhari

Ma'aikatan jinyar sun kuma bayyana cewa sun yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnati don jin inda aka kwana ta hanyar tura wasiƙu amma har yanzu babu wata amsa.

Matsalar da yajin ma'aikatan za ta haifar a Kano

Idan har wannan yajin aiki ya tabbata, za a samu babban cikas a harkokin kiwon lafiya, wanda zai shafi marasa lafiya da asibitocin Kano.

Har kawo yanzu dai gwamnatin Kano ba ta ce komai ba dangane da wa'adin da ma'aikatan jinyar suka bayar ba, cewar rahoton Tribune.

Kotu za ta yi hukunci kan gyara fadar Nassarawa

A wani labarin kuma babbar kotun Kano ta zabi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a ƙarar da aka nemi dakatar da gyara fadar Nassarawa.

Gwamnatin Kano ta buƙaci kotun ta hana Sarki na 15, Aminu Ado Bayero aiwatar da shirinsa na gyaran fadar da yake ciki yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262