'Yan Boko Haram Sun Yi Ta'addanci a Borno Ana Murnar Samun 'Yancin Kai
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi garkuwa da wasu manoma a jihar Borno bayan sun kai musu farmaki a gona
- Miyagun ƴan ta'addan sun yi wa wasu daga cikin manoman yankan rago bayan sun tafi da su zuwa sansaninsu
- Harin da ƴan Boko Haram suka kai a ƙaramar hukumar Gwoza ya kuma yi sanadiyyar rasa ran wani jami'in tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun kashe aƙalla manoma biyar a wani mummunan hari a jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a ƙauyen Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Ƴan Boko Haram sun yi ta'asa a Borno
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun yanka biyar daga cikin manoman da suka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ta'addan sun farmaki manoman ne yayin da suke tsaka da gudanar da aiki a gona.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kashe wani jami’in rundunar ƴan sa-kai ta CJTF, Jubril Zarana, wanda ya haɗa kai da jami’an tsaro wajen daƙile harin.
"Cikin alhini muke sanar da sace kimanin manoma 15 da suka haɗa da yara, mata, matasa da tsofaffi da ƴan ta’addan Boko Haram suka yi a Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza."
"Bayan ƴan ta’addan sun kai mutanen zuwa sansaninsu sun yi wa mutane biyar yankan rago waɗanda suka haɗa da Isa Musa Moh’d Diyara, Doglas, Salawuddin Suleman Dauda Lawan, Maryam Gwambran, Matan Kaka Mobil Aga da Baba Amos."
"Daga baya ƴan ta’addan na Boko Haram sun sako mata uku daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su."
- Wata majiya
Sojoji sun ceto mutane a hannun ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar ceto mutane 40 da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng