An Zargi Sanata da Biyawa dan Ta'adda Kujerar Hajji, DSS Ta Fara Bincike

An Zargi Sanata da Biyawa dan Ta'adda Kujerar Hajji, DSS Ta Fara Bincike

  • Jami'an DSS sun fara binciken Sanata Shehu Buba bisa zargin alaka da rikakken dan ta'adda Abubakar Idris
  • An gano alamun alaka tsakanin Sanatan da Abubakar bayan hadiminsa Yahaya Ibrahim ya biyawa dan ta'addan aikin hajji
  • Zuwa yanzu, an cafke Abubakar Idris, sannan an mika rahoto kan Sanata Shehu Buba ga shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta fara binciken Sanata mai wakiltar ta Kudu a majalisar dattawa, Shehu Buba da alaka da ta'addanci.

Ana zargin Sanata Shehu Buba da alaka da rikakken dan ta'adda, Abubakar Idris, kuma tuni aka mika bayanin ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da murnar ranar ƴanci: Gwamnatin tarayya ta karawa ƴan fansho albashi

Sen Shehu Buba Umar
Ana zargin Sanata da daukar nauyin ta'addaci Hoto: Sen Shehu Buba Umar
Asali: Facebook

Arise news ta wallafa cewa an hada cikakken rahoton tsaro kan Sanatan bayan gano wasu kwararan dalilan da ke nuna ya na da alaka da dan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Sanata da daukar nauyin ta'adda

Jaridar Thisday ta wallafa cewa an gano Sanata Shehu Buba ya biyawa dan ta'adda Abubakar Idris kudin aikin hajji ta hannun daya daga cikin hadimansa.

Majiyar gidan talabijin ta bayyana cewa lamarin ya sa jami'an DSS su ka kutsa ofishin hukumar aikin hajjin jihar Bauchi domin zurfafa bincike.

Alaka da Sanata: DSS sun kama dan ta'adda

Zuwa yanzu dai jami'an DSS sun cafke dan ta'adda Abubakar Idris da ake zargin Sanatan Bauchi ya dauki nauyinsa zuwa aikin hajjin bara.

An yi zargin Yahaya Ibrahim, wani babban hadimin Sanata Shehu Buba ne ya yi wa dan ta'addan da ake zargi da kai hare-hare Zamfara da wasu sassa rajista.

Kara karanta wannan

Rikici ya rincabe tsakanin dabar yan ta'adda 2, rayuka sun salwanta

Dan ta'adda ya cika baki bayan kashe abokinsa

A baya mun wallafa cewa fitinannen dan ta'adda, Bello Turji ya ce kisan abokin burminsa, Halilu Sububu da da sojoji su ka yi bai girgiza shi ba balle ya ba shi tsoro.

A wani bidiyo da ya fitar bayan kisan mai gidansa, Bello Turji ya yi ta'aziyyar Sububu, sannan ya bugi kirji kan cewa babu abin da sojojin su ka yi da zai tsorata shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.