‘Ba a Saurare Shi ba,’ Yadda aka yi Rubdugu ga Tinubu kan Jawabin 1 ga Watan Oktoba

‘Ba a Saurare Shi ba,’ Yadda aka yi Rubdugu ga Tinubu kan Jawabin 1 ga Watan Oktoba

  • A ranar 1 ga watan Oktoba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa kan yanci da aka samu daga turawan Birtaniya
  • Sai dai jawabin shugaban kasar na wannar shekarar ya jawo suka sosai kan cewa bai yi magana kan manyan damuwowin Najeriya ba
  • Kungiyoyin fararen hula da manyan yan siyasa ne suka yi zazzafan martani ga shugaban kasar kan jawabin ranar yanci da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi bayan Najeriya ta cika shekaru 64 da samun yancin kai.

Yan Najeriya sun yi caccaka ga shugaban kasar kan jawabin da ya yi inda suka ce shugaban kasar bai yi abin da ya kamata ba.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Bola Tinubu
An yi martani kan jawabin Tinubu na Oktoba. Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyoyin fararen hula na cikin waɗanda suka yi raddi ga shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ka canza salo' - Rafsanjani ga Tinubu

Wani shugaban kungiyoyin fararen hula, Auwal Musa Rafsanjani ya ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta canza salon gudanar da mulki.

Rafsanjani ya ce maimakon jawabi, yan Najeriya suna son ganin tsare tsaren da za su kawo musu sauƙin rayuwa ne a kan halin da suke ciki.

Atiku ya ce ba a saurari Tinubu ba

A cikin martanin da Atiku Abubakar ya yi, ya ce yan Najeriya ba su da lokacin sauraron jawabin Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yan Najeriya suna can suna fama da wahalar rayuwa da gwamnatin Tinubu ta kawo.

Jam'iyyar LP ta yi wa Tinubu kaca-kaca

Shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure ya ce ya kamata yan Najeriya su hada kai su ceto kasar daga hannun yan son zuciya.

Kara karanta wannan

'Babu abin da ya dame mu': Turji ya fito ya cika baki kan kisan Halilu Sububu

Julius Abure ya ce dole a hada kai a ceto Najeriya daga masu maguɗin zaɓe, matsalar rashin tsaro da talauci.

Tinubu ya ce an kashe yan ta'adda 300

A wani rahoton, kun ji cewa yayin jawabin ranar yanci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce an kashe yan ta'adda sama da 300 a shekara daya.

Bola Ahmed Tinubu ya ce sojojin Najeriya sun samu nasarar dawo da zaman lafiya a kauyuka da dama kuma mutane sun koma gidajensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng