Ana Batun Bincikensa El Rufai Ya Bayyana Lokacin da Zai Yi Ritaya daga Siyasa

Ana Batun Bincikensa El Rufai Ya Bayyana Lokacin da Zai Yi Ritaya daga Siyasa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya nesanta kansa daga shirin yin ritaya daga harkokin siyasa
  • El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan babu shirin yin ritaya a tattare da shi kuma zai dawo siyasa a 2027 bayan kammala karatunsa
  • Malam El-Rufai ya kuma musanta zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa inda ya ce a shirye yake ya yi rantsuwa da Kur'ani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi magana kan lokacin zai yi ritaya daga siyasa.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan ba shi da shirin yin ritaya daga harkokin siyasa.

El-Rufai ya fadi lokacin ritaya daga siyasa
El-Rufai ya ce ba zai yi ritaya daga siyasa ba Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Nasir El-Rufai bai da shirin ritaya daga siyasa

Kara karanta wannan

"Na shirya rantsewa da Alƙur'ani ban taɓa satar ko kwabo ba," Tsohon gwamna El Rufai

Jaridar The Punch ta rahoto cewa El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon Freedom da ke Kaduna a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana siyasa a matsayin mutu ka raba, yana mai cewa zai dawo siyasa a shekarar 2027.

"Ina da niyyar komawa siyasa a 2027 bayan na kammala karatuna. Babu ritaya a siyasa. Da yardar Allah za mu dawo mu ci gaba da yi wa jama’a hidima."

- Malam Nasir El-Rufai

El-Rufai ya musanta zargin cin hanci

El-Rufai ya kuma musanta zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa inda ya ce a shirye yake ya rantse da Al-Kur’ani, ya kuma ƙalubalanci magabatansa da shugabannin da ke kan mulki yanzu da su yi hakan.

Tsohon gwamnan ya musanta zargin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi cewa an sace ko kuma an karkatar da N423bn a ƙarƙashinsa lokacin da yake matsayin gwamnan jihar, rahoton Leadership ya tabbatar da wannan.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Zanga zangar da ake shrin yi ta gamu da tangarɗa a Kaduna

El-Rufai ya yi nuni da cewa ana zargin gwamnatinsa ne ba tare da kawo wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, sannan hukumomin EFCC da ICPC na farautar na kusa da shi.

"Yadda na ji bayan dawo da Sanusi II", El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi magana kan dawowa da Muhammadu Sanusi II kan sarautar Sarkin Kano.

Nasir El-Rufai ya ce dawo da Mai martaba Muhammadu Sanusi II kan sarauta na daya daga cikin abin da ya fi faranta masa rai a rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng