"Kar a Karaya:" Goodluck Jonathan Ya Tura Sakon Karfafa Gwiwa ga Yan Kasa

"Kar a Karaya:" Goodluck Jonathan Ya Tura Sakon Karfafa Gwiwa ga Yan Kasa

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya taya yan kasa murnar zagayowar ranar samun yancin kai
  • Jonathna ya ce duk da tarin matsalolin da ake fuskanta, bai dace yan kasa su karaya da samun cigaba ba
  • Tsohon shugaban ta sanarwar da hadiminsa, Ikechukwu Eze ya fitar, ya ce akwai fatan samun nasara a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya karfafi yan kasar nan a dai-dai lokacin da aka cika shekaru 64 da samun yanci.

Dr. Jonathan ya shawarci yan kasa da ka da su karaya da halin da kasa ke ciki a yau.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Bayan lissafo matsaloli, gwamna ya fadi abin da ake bukata daga yan Najeriya

Jonathan
Tsohon shugaba Jonathan ya yi murnar cikar Najeriya shekaru 64 da samun yanci Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tsohon shugaban ya ce duk da halin da ake ciki mai dimbin kalubale, bai kamata a karaya da gina kasa cike da arziki da kwanciyar hankali ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata a yabawa mazan jiya da su ka sadaukar da kawunasu saboda tabbatar da yancin Najeriya.

Goodluck Jonathan ya ba yan kasa shawara

Jaridar Independent Newspaper ta tattaro tsohon shugaba, Goodluck Jonathan ya amince akwai manyan matsaloli da ke addabar kasa da mazauna cikinta.

Ta cikin sanarwar da hadiminsa, Ikechukwu Eze ya fitar, Dr. Jonathan ya ce amma wannan ba dalili ne za a karaya da samun sauki ba.

Jonathan: "Yau ranar murna ce a Najeriya"

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce yau rana ce da za a jinjinawa magabata da su ka yi fafutukar kwato yancin Najeriya daga turawa.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: An gano illolin talauci, kungiya ta kawowa Tinubu shawara

Shugaban ya shawarci kasar ta dabbaka al'adar dimokuradiyya da riko da gaskiya wajen tabbatuwar cigaba mai dorewa.

Gwamna ya taya kasa murnar yanci

A baya mun wallafa cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya taya yan kasar nan murnar cika shekaru 64 da samun damar mulkar kanta daga turawa.

Ya shawarci yan kasa su taimakawa shugabannin Najeriya da addu'a domin samun damar sauke nauyin jama'a na tabbatar da tsaro da cigaban tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.