1 ga Oktoba: Abin da Ke Faruwa a Kano bayan Fara Zanga Zanga a Wasu Sassan Najeriya
- Mutanen Kano sun kauracewa zanga-zangar da ake yi ranar Talata 1 ga watan Oktoba a wasu sassan ƙasar nan
- Rahotanni sun nuna wasu daga cikin mazauna jihar Kano sun yi zamansu a gida yayin da wasu kuma suka fita harkokinsu
- Amma wani matashi a Kano ya shaidawa Legit Hausa wasu sun fita sai dai ƴan sanda sun gano shirunsu, sun cafke su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Mazauna jihar Kano sun yi fatali da zanga-zangar da ake yi yau 1 ga watan Oktoba, 2024 kan tsadar rayuwa da yunwa a faɗin ƙasar nan.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen Kano sun ƙauracewa fita kan tituna a wannan karon, sun ci gaba da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.
Zanga-zanga: Abin da ke faruwa a Kano
Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa sakamakon ayyana wannan rana a matsayin ranar hutu, da yawa mutanen Kano musamnan ma'aikata su zaɓi zama a gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan zanga-zanga da ake yi a wasu jihohi mai taken “FearlessInOctober" ta yaɗu ne a kafafen sada zumunta, watanni buyu bayan zanga-zangar da aka yi a Agusta.
An shiya duka zanga-zangar ne domin nuna adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu, inda matasa suka nemi a dawo da tallafin mai.
Duk da abubuwan da suka faru na ɓarna da sace-sace a zanga-zangar watan Agusta, wannan karon Kanawa sun ce ba za a sake yaudararsu ba.
Kano: Mutane sun ci gaba da harkokinsu
An tataro cewa babu hayaniya a manyan tituna sannan babu cunkoson ababen hawa, yayin da masu shaguna da sauran kananan sana'o'i suka ci gaba da harkokinsu.
Binciken da aka yi a manyan kasuwanni kamar Kwari, Sabon Gari, Mawaka da Kurmi ya nuna cewa galibin ƴan kasuwa sun buɗe shaguna, ‘yan kalilan ne a rufe.
Legit Hausa ta tuntuɓi wani matashi a Kano, Sanusi Isiyaku, wanda ya shaida mana cewa babu wata zanga-zanga da ke wakana yau, mutane sun yi zamansu a gida.
Ƴan sanda sun kama wasu a Kano
Sanusi ya ce matasa sun yi zamansu a gida, wasu kuma sun buɗe wuraren kasuwancinsu, sai dai duk da haka wasu marasa ji sun fita zanga-zanga.
A cewarsa, ana zargin wasu mutane suka ɗauki nauyin matasan da suka fita, kuma nan da nan ƴan sanda suka cafke su bayan gano manufarsu.
"Mu na zaune lafiya wannan karon, matasa sun yi zamansu a gida, na samu labarin akwai wasu ƴan ƙungiyoyi da suka fita to amma ƴan sanda suk cafke su bayan samun bayanan sirri," in ji shi.
Yan sanda tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zanga a Abuja sun gamu da cikas yayin da 'yan sanda suka rika jefa masu barkonon tsohuwa
A ranar Talata, 1 ga watan Oktoba ne matasa suka fara gudanar da zanga zangar nuna adawa da tsadar fetur, kayan abinci da na masarufi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng