Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Gargadi Tinubu kan Manakisar Kwankwaso
- Tsohon kwamishina a mulkin Abdullahi Ganduje ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan alaka da Rabiu kwankwaso
- Jigon APC, Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce hadaka da tsohon gwamnan sai an yi taka tsan-tsan saboda zai iya cin amana
- Hakan na zuwa ne bayan rade-radin cewa ana zama domin hadaka saboda ba Kwankwaso mukamin Minista a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jigon APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya gargadi Bola Tinubu kan halin Rabiu Kwankwaso.
Jigon APC na magana ne bayan rade-radin cewa Kwankwaso zai yi hadaka da APC domin samun mukamin Minista.
An gargadi Tinubu kan hadaka da Kwankwaso
Ilyasu Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin zantawa da yan jaridu a Kano inda ya ce Kwankwaso ba abin yarda ba ne, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishinan ya ce an samu bayanai cewa Kwankwaso na ganawa da Tinubu domin hadaka da APC.
Ya ce ya kamata Tinubu ya yi hankali da Kwankwaso saboda ba shi da tabbas musamman wurin rike amana.
Kwankwaso: Jigon APC ya ja kunnen Tinubu
"Akwai bayanai cewa Tinubu yana ganawa da Kwankwaso domin hadakar NNPP da APC, ya kamata a yi hankali kan haka."
"Ya kamata Tinubu ya hada da jiga-jigan APC a Kano cikin ganawar da suka hada da Sanata Barau da Ado Doguwa da Abdullahi Abbas har ma Abdullahi Ganduje."
"Dalilin fadan haka kuwa, na san wanene Kwankwaso, ba abu mai wahala ba ne ya ci amanar Bola Tinubu saboda haka kasancewar 'yan APC za su zama shaidu."
- Musa Ilyasu kwankwaso
Kwankwaso ya mgantu kan hadakar NNPP-PDP
Kun ji cewa tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan hadakar jiga-jigan jam'iyyun adawa game da zaben 2027.
Kwankwaso ya ce Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suna bata lokacinsu ne kan shirin kifar da Bola Tinubu ne.
Wannan na zuwa ne yayin da jiga-jigan jam'iyyun adawa suke shirin haɗaka ta musamman domin shirin zaben 2027 mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng