Najeriya @64: Yadda Bikin Ranar Samun Ƴanci Ke Gudana Kai Tsaye, Tinubu Ya Yi Jawabi

Najeriya @64: Yadda Bikin Ranar Samun Ƴanci Ke Gudana Kai Tsaye, Tinubu Ya Yi Jawabi

Abuja - A yau Talata, 1 ga watan Oktoba, 2024 Najeriya ke bikin zagayowar ranar samun ƴancin kai daga turawan karo na 64 a tarihi.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi kai tsaye ga ƴan Najeriya da misalin karfe 7:00 na safiya.

Shugaba Tinubu.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi jawabi kai tsaye Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugaban ya yi magana kan muhimman batutuwa da suka shafi ƴan ƙasa musamman halin ƙunci da matsalar tsaro, inda ya ba da tabbacin komai zai wanye.

Yayin da shagalin bikin wannan rana ya fara kankama, Legit Hausa ta shirya tsaf za ta kawo maku abubuwan da ke faruwa kai tsaye.

Tinubu ya magantu kan hadin kan kasa

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin samar da hadin kan kasa da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya kuma jaddada mahimmancin kasuwanci da saukin gudanar da shi, tare da karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su jajurce a kan ci gaban kasar domin samun kyakkyawar makoma.

Tinubu ya magantu a kan karfafa matasa

Shugaba Tinubu ya ce za a gudanar da taron matasa na kasa na kwanaki 30 domin magance kalubale da damarmakin da matasan Najeriya ke fuskanta.

Hakazalika ya ce an samar da shirin 3MTT domin samar da kwararrun matasa kan fasa a kasar, yayin da asusun ba da lamunin karatu (NELFUND) ke ba da rancen kudi ga ɗalibai.

Tinubu yayi magana kan sauyin makamashi

Shugaba Tinubu ya ce kokarin gwamnatinsa a kan iskar gas din CNG domin ganin ya isa lungu da sakon kasar nan ya na ci gaba da tabbata.

Ya ce gwamnatin tarayya tana kuma taimaka wa jihohi wajen samun motocin CNG domin sufurin jama'a cikin farashi mai rahusa.

Tinubu yayi magana a kan cigaban noma

Tinubu ya ce gwamnati na zuba jari wajen noman zamani, da samar da taki da tarakta ga manoma a fadin kasar.

Ya ce, za a kafa wata cibiyar hada taraktoci na John Deere guda 2000 da sauran kayan aikin gona.

Tinubu ya magantu kan tsaro da yakar ta'addanci

Shugaba Tinubu ya ce ana samun nasara a yaki da ta’addanci da ‘yan bindiga, inda aka kawar da kwamandojin Boko Haram da ‘yan bindiga sama da 300 kwanan nan.

Ya kara da cewa an samar da zaman lafiya ga daruruwan garuruwan Arewa, wanda hakan ya ba dubban mutane damar komawa gida.

Tinubu ya yi magana kan gyaran tattali

Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki domin rage radadin rayuwa da kuma inganta 'yan kasar.

A cewarsa, jarin da aka zuba kai tsaye daga ketare ya kai sama da dala biliyan 30 a shekarar da ta gabata.

Shugaban ya kara da cewa gwamnati ta biya bashin dala biliyan bakwai da aka gada tare da kawar da basussukan da ya haura naira tiriliyan 30.

Muhimman abubuwa daga jawabin Tinubu

Ga takaitaccen jawabin ranar samun ‘yancin kai na shugaba Tinubu:

Waiwaye kan shekaru 64 na 'yancin kan Najeriya.

Tinubu ya ce yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, akwai bukatar a yi tunani a kan ci gaba da kuma kalubalen da kasar ke fuskanta.

Duk da cewa ana fama da rikice-rikice da dama, ya ce Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa mai karfi, hadin kai, kuma mai cin gashin kanta.

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.