Shugaba Tinubu Ya Damu da Matasa, Ya Shirya Yin Taron Kasa na Kwanaki 30
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce za a gudanar da taron matasa na kwanaki 30 domin nemo mafita kan matsalolinsu
- Ya ce za a dora alhakin zakulo matasan da za su halarci taron na kasa a wuyan wakilansu da ke gwamnati
- Ana sa ran nusar da matasan muhimmmancin tafiyarsu a gwamnati da bayar da gudunmawa wajen cigaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa za a gudanar da gagarumin taron matasa na kasa inda za a tattauna da masu ruwa da tsaki.
A jawabinsa na ranar samun yanci a safiyar Talata, shugaban ya ce za a duba duk wasu matsaloli da kalubale da matasan kasar nan ke fuskanta.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban ya ce za a shafe kwanaki 30 ana tattaunawa domim samarwa matasan Najeriya mafita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya fadi dalilin taron matasa
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce za a gudanar da taron matasa na kwanaki 30 domin karfafa masu gwiwa wajen tallafawa gina kasa.
Ya ce za a bullo da hanyar tabbatar da an rika sa matasa cikin harkokin gwamnati da fito da tsare-tsaren da za su inganta rayuwarsu.
Tinubu zai tattaro matasan Najeriya
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a tattaro matasa daga sassan kasar nan daban-daban domin a tattauna mafita kan matsalolinsu.
Ya ce za a zabo matasan da za su halarci taron na kwanaki 30 ta hanyar aiki tare da wakilansu a gwamnatin Najeriya.
Matasa sun yi mamakin taron kwana 30
Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula a Kano, Ambasada Ibrahim Waiya kuma shugaban kwamitin zaman lafiya na Kano ya ce sun yi mamakin tsayin kwankin da shugaban kasa ya ce za a yi taro.
Ya ce amma babu mamaki akwai manufar da ake so a cimma na cigaban matasa a taron da za a gudanar na nemawa jama'a mafita.
Matasa na adawa da manufofin Tinubu
A baya mun ruwaito cewa kungiyar 'Northern Youth Council of Nigeria' ta ayyana shirinta na gudanar da zanga-zangar kwana daya domin nuna adawa da yunwa a kasar nan.
Za a gudanar da zanga-zangar a ranar Talata, 1 Oktoba 2024 domin nunawa gwamnatin tarayya rashin jin dadi kan yadda aka yi biris da yan Najeriya cikin talauci da rashin tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng