Ranar Ƴanci: Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Farashin Kayan Abinci, Ya Faɗi Mafita

Ranar Ƴanci: Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Farashin Kayan Abinci, Ya Faɗi Mafita

  • Bola Ahmed Tinubu ya ƙara tabbatarwa ƴan Najeriya duk wahalar da suke kuka a kai za ta wuce kuma daɗi na nan tafe
  • Shugabar ƙasar ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi domin abinci ya wadata da kuma rage farashinsa a ƙasar nan
  • Shugaba Tinubu ya yi wannan furuci ne a jawabin da ya yi kai tsaye ga ƴan Najeriya ranar 1 ga watan Oktoba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara lallashin ƴan Najeriya, ya ce nan ba da jimawa ba wahala za ta wanye kuma za su samu walwala da jin daɗi.

Bola Tinubu ya kuma buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kai wuri guda, kana su jajirce wajen gina ƙasar da kowa ke buri.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yancin kai: Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya, an samu bayanai

Shugaba Tinubu Tinubu.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su kara jajircewa domin farin ciki da walwala na tafe Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a jawabinsa na ranar bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴancin kai daga turawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Olusegun Dada ne ya wallafa cikakkken jawabin Tinubu a shafinsa na manhajar X.

Bola Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya su jure

Tinubu ya aminta da cewa hanyar da ya ɗauko cike take da ƙalubale da wahala, yana mai rokon al'umma ta ba gwamnatinsa haɗin kai wajen magance matsaloli.

"Ƴan uwana ƴan Najeriya, ku sani ranakun farin ciki da walwala na tafe, ya kamata ƙalubalen da muke ciki ya ƙara mana kwarin guiwa, mu ƴan Najeriya ne, muna da juriya da jajircewa.

- Bola Tinubu.

Tinubu zai rage tsadar abinci a Najeriya

Shugaban ya kuma bayyana cewa gwammatinsa za ta yi kokarin sauke farashin kayayyakin abinci, wanda tashinsa ya ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahala.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gano matsalolin da suka hana Najeriya samun ci gaba

A cewarsa, gwamnatinsa ta tashi tsaye haiƙan domin dawo da zaman lafiya musamma a Arewa ta yadda manoma za su ci gaba da harkokinsu na noma.

"Muna sa ran abinci zai wadata a ƙasa kuma farashinsa zai yi arha, na yi muku alkawarin cewa ba za mu yi ƙasa a guiwa ba kan wannan," in ji Tinubu.

Najeriya ta roki China ta yafe mata bashi?

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta ce ba a tattauna batun yafewa Najeriya bashi ba a ganawar Bola Tinubu da Xi Jinping.

Ministan harkokin kasar waje, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan, ya ce China a shirye take ta ba Najeriya ƙarin bashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262