Najeriya @64: Abin da Tinubu Ya Fada game da Halin Kunci, Ya Roki Yan Kasa

Najeriya @64: Abin da Tinubu Ya Fada game da Halin Kunci, Ya Roki Yan Kasa

  • Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi jawabi mai kama hankali ga yan kasar kan halin kunci da ake ciki
  • Tinubu ya ce tabbas ana cikin wani hali kuma za a iya fuskantar kalubale a gaba amma komai zai dawo dai-dai
  • Shugaban ya roki yan Najeriya da su cigaba da nuna juriya da kuma hakuri yadda suka saba domin kawo sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Tinubu ya ce tabbas ana cikin halin kuci a Najeriya amma za a ci moriya a gaba cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Gwamna ya lissafo ni'imomi 3 a kasar nan, ya nemi a dage da addu'a

Tinubu ya roki yan Najeriya kan halin kunci da ake ciki
Bola Tinubu ya ba da tabbacin fita daga kangin da ake ciki a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

Tinubu ya magantu kan halin matsi a Najeriya

Shugaban ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga yan Najeriya a yau Talata 1 ga watan Oktoban 2024 da hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce dole za a fuskanci kalubale da dama inda ya bukaci hadin kan yan kasa domin kawo sauyi.

Ya bukaci yan Najeriya da su cigaba da nuna juriya da kuma ba shi hadin kai domin kawo sauyi mai inganci a Najeriya baki daya.

Halin kunci: Tinubu ya roki yan Najeria

"Yan uwana yan Najeriya, tabbas dadi na gaba, kalubalen da muke fuskanta za su kara ba mu tabbacin yarda da kan mu ne."
"Mu yan Najeriya ne da ke da kwarin guiwa da kuma kokari da juriya, kullum mu na cin galaba kan kalubalen da muke samu."

Kara karanta wannan

'Ka yi hankali,' Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu kan korar ministoci

"Ina rokonku da ku yi imani da tsare-tsarenmu, za mu yi mai yiwuwa domin inganta kasa, idan muka hada kai, tabbas za mu samar da cigaba da daraja ga Najeriya."

- Bola Tinubu

Tinubu ya shawarci yan Najeriya kan karancin abinci

Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya kan yadda za a shawo kan tsadar kayan abinci a kasar.

Tinubu ta bakin hadiminsa, ya ce akwai bukatar kowa ya natsu ya ba da gudunmawa wajen gina kasa, musamman duba da yanayin da ake ciki.

Tun bayan hawan Tinubu mulki ake samun kalubalen cigaban tattalin arziki da kuma tashin farashin kayayyaki a kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.