Asiri Ya Tonu: An Kama Basarake da Wasu Mutum 12 bisa Zargin Garkuwa da Kisan Kai

Asiri Ya Tonu: An Kama Basarake da Wasu Mutum 12 bisa Zargin Garkuwa da Kisan Kai

  • Dakarun ƴan sanda sun cafke basarake da wasu mutum 12 da ake zargi da sace mafarautan ruwa uku tare da hallaka su a jihar Akwa Ibim
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, Joseph Eribo ya ce waɗanda ake zargin sun datse kawunan mafarautan tare da binne gawarwakinsu a daji
  • Ya ce bayanan sirrin da ƴan sanda suka samu ya nuna dagacin ne ya sa sauran aikata wannan ɗanyen aiki domin yin asiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Ƴan sanda sun cafke dagacin kauyen Utit Antai da ke ƙaramar hukumar a jihar Akwa Ibom, Okon Asuquo Etteokpo bisa zargin garkuwa da kisan kai.

Jami'an ƴan sandan sun damke basaraken tare da wasu mutum 12 da ake zargi da sace wasu mafarautan ruwa uku tare da yi masu yankan rago a Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

"PDP ce sila," Jam'iyyar APC ta bayyana muhimmin aikin da ya cinye shekarun mulkin Buhari

Dakarun ƴan sanda.
Yan sanda sun cafke basarake bisa zargin hannu a garkuwa da kisan mafarauta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Punch ta tattaro cewa waɗanda ake zargin sun sace mafarautan, suka datse masu kawuna sannan suka binne su a jeji bisa umarnin dagacin kauyen da nufin yin asiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan sanda suka kama barasake a Akwa Ibom

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Joseph Eribo ne ya bayyana haka a wata hira da menama labarai yayin nuna waɗanda ake zargin a birnin Uyo ranar Litinin.

Ya ce ƴan sanda sun kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna an kashe mafarautan tare da binne su a cikin jejin tsakanin kauyukan Efiat da Unyenge.

Ya ce bayan kama wadanda ake zargin, dakarun ƴan sanda suƙa zurfafa bincike wanda a karshe suka samu gargwakinsu a kaburbura marasa zurfi, an cire masu kai.

Ƴan sanda sun cafke masu hannu a kisan

"Bayanan da aka tattara sun nuna cewa masu garkuwan sun yada zango ne a wani dajin da ke tsakanin kauyukan Efiat da Unyenge a ƙaramar hukumar Mba.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Kotu ta yanke hukunci kan zanga zangar da ake shirin yi, ta jero wurare 4

"Nan take bayan samun wannan bayanai, jami’an rundunar suka kewaye dajin kuma suka kama wadanda ake zargin,” in ji Eribo.

Kwamishinan ƴna sanda ya ƙara da cewa an kwato kusan kwalaye 15 na alburusai masu rai daga hannun wadanda ake zargin, rahoton The Cable.

Ya lissafinsu aunayensu wadda ya haɗa da Jephter Inwang, Clement Emmanuel, Promise Nkerobia, Anthony Atte, Nkereuwem Edet da Joseph Asuquo da sauransu.

Sojoji sun ƙara hallaka ƴan ta'adda

A wani rahoton kuma rundunar sojin Najeriya ta gwabza kazamin fada da yan ta'adda a jihohi daban daban kuma ta samu nasarar hallaka su.

Bayan gwabza fadan, sojojin Najeriya sun ceto mutanen da yan bindigar suka kama cikin jeji, kimanin mutum 40 sun kubuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262