1 ga Oktoba: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi, Ta Jero Wurare 4

1 ga Oktoba: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi, Ta Jero Wurare 4

  • Babbar kotun Ogun ta taƙaita zanga-zangar da ake shirin yi ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 zuwa wurare huɗu kaɗai a jihar
  • Kotun ta kuma umarci kwamishinan rundunar ƴan sanda ya tabbatar da an bi wannan umarni wanda zai shafe mako guda yana aiki
  • Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Ogun ne ya shigar ƙara gaban kotun domin taƙaita wuraren zanga-zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Wata babbar kotu mai zama a Abeoukuta ta taƙaita zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa zuwa wurare huɗu kaɗai a jihar Ogun.

Wannan hukuncin da kotun ta yanke na nufin waɗannan wurare huɗu kaɗai aka amince matasa su gudanar da zanga-zangar da suka shirya ranar 1 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta gargaɗi mutanen Kano kan zanga zangar da ake shirin yi

Masu zanga-zanga.
Kotu ta taƙaita zanga-zangar da ake shirin yi ranar 1 ga watan Oktoba a Ogun Hoto
Asali: Twitter

Wurare 4 da aka amince da yin zanga-zanga

Channels tv ta ce wuraren da kotun ta taƙaita zanga-zangar sun haɗa da babban filin wasa na Moshood Abiola da ke Abeokuta da filin kwallon Gatewa a Sagamu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran su ne filin kwallon Dipo Dina da ke Ijebu Ode da kuma makarantar Comprehensive High da ke garin Ota.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Tajudeen A. Okunsokan ta yanke wannan hukunci a ƙara mai lamba AB/667/2024, da Antoni Janar na jihar Ogun, ya shigar.

Waɗanda ake ƙara sun ƙunshi kungiyoyin da ke sahun gaba wajen shirya wannan zanga-zanga da wasu ɗaiɗaikun mutane.

Bisa wannan umarni na kotun dai an wajabtawa masu zanga-zangar kar su taru a ko ina sai wuraren da aka keɓe masu a faɗin jihar Ogun.

Kotu ta ba kwamishinan ƴan sanda umarni

Kotun ta kuma umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya tabbatar da aiwatar da hukuncin, wanda zai shafe kwanaki bakwai yana aiki, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Zanga zangar da ake shrin yi ta gamu da tangarɗa a Kaduna

Mai shari'a Taudeen ya ce umarnin takaita zanga-zangar zai shafe kwanaki bakwai yana aiki kamar yadda doka ta 39 ta tanada a kundin dokokin babbar kotun Ogun.

Ƴan sanda sun gargaɗi mazauna Kano

Ku na da labarin rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta girke jami'anta a wurare daban-daban domin daƙile duk wata barazana daga masu zanga-zanga.

Mai magana da yawun ƴan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ba za ta yarda a maimaita abin da ya faru a watan Agusta ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262