Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Roƙon Kasar China Ta Yafewa Najeriya Bashi

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Roƙon Kasar China Ta Yafewa Najeriya Bashi

  • Gwamnatin tarayya ta ce ba a tattauna batun yafewa Najeriya bashi ba a ganawar Bola Tinubu da shugaban China, Xi Jinping
  • Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan, ya ce China a shirye take ta ba Najeriya ƙarin bashi
  • Ambasada Yusuf Tuggar ya ce Najeriya ba ta cikin jerin ƙasashe masu tasowa waɗanda tarin basussuka ya yi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ƙasar China a shirye take ta ƙara ba Najeriya bashin kuɗi domin zuba su a fannin gina ayyukan raya kasa.

Gwamnatin ta kuma musanta raɗe-raɗin cewar Najeriya ta fara roƙon China ta yafe mata wasu daga cikin basussukan da take bin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gano matsalolin da suka hana Najeriya samun ci gaba

Ambasada Yusuf Tuggar.
Gwamnatin tarayya ta ce China a shirye take ta karawa Najeriya bashin kuɗi Hoto: Yusuf Tuggar
Asali: UGC

Ministan harkokin waje, Ambasada Tuggar ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Bashi bai yi wa Najeriya yawa ba'

Ya ƙara da cewa Najeriya ba ta cikin jerin kasasshen da ke cikin haɗari saboda yawan basussuka, kamar yadda Leadership ta kawo.

A cewar ofishin kula da basussuka (DMO), bashin da ake bin Najeriya zuwa watan Maris na 2024 ya kai N56trn ($42bn) yayin da bashin cikin gida kuma ya kai N65trn ($46.29bn).

Da aka tambaye shi ko Najeriya ta fara rokon a yafe mata wasu basussuka a lokacin gawagar shugaba Bola Tinubu da shugaban China, Xi Jinping, ministan ya ce ko kaɗan babu wannan batun.

Tinubu ya roƙi China ta yafewa Najeriya bashi?

Yusuf Tuggar ya ce ba a tattauna batun yafewa Najeriya basussuka a zaman Tinubu da shugaban China ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dauki barazanar ASUU da gaske, ta fara daukar mataki

Tribune ta ruwaito ministan na cewa:

"Ko kaɗan hakan ba ya cikin abubuwan da muka tattauna da China, idan ana maganar bashi, ku duba ku gani Najeriya ba ta cikin ƙasashen da bashi ya yi wa katutu.
"Idan ana maganar bashin kasashe masu tasowa, Nijeriya ba ta cikin wannan mawuyacin hali. A gaskiya ma, kasar Sin a shirye take ta kara ba mu rance."

Tinubu zai yiwa ƴan Najeriya jawabi

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ƴan Najeriya a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024.

A cikin wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ya ce shugaban ƙasan zai yi jawabin ne da ƙarfe 7:00 na safe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262