Rundunar Ƴan Sanda Ta Gargaɗi Mutanen Kano kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

Rundunar Ƴan Sanda Ta Gargaɗi Mutanen Kano kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta girke jami'anta a wurare daban-daban domin daƙile duk wata barazana daga masu zanga-zanga
  • Mai magana da yawun ƴan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ba za ta yarda a maimaita abin da ya faru a watan Agusta ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa ranar 1 ga watan Oktoba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi masu shirin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

Rundunar ta ja kunnen masu shirin fita kan tituna da cewa ba za ta lamunci karya doka da oda da sunan zanga-zangar tsadar rayuwa ba.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Zanga zangar da ake shrin yi ta gamu da tangarɗa a Kaduna

SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Yan sanda sun gargaɗi masu shirin fita zanga-zanga ranar 1 ga watan Oktoba a Kano Hoto: SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi wannan gargadin a madadin kwamishinan ‘yan sandan, CP Salman Dogo Garba, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Ƴan sanda za su ɗauki mataki

SP Kiyawa ya yi gargadin cewa rundunar ta ɗauki darasi abin da ya faru na ɓarna da tada zaune tsaye a zanga-zangar da ta gabata a fadin kasar nan, rahoton Channels tv.

Ya ce dakarun ƴan sanda za su ɗauki matakai, ba za su sake bari a maimaita abubuwan da suka faru na sace-sacen dukiyar al'umma da lalata kayan gwamnati ba.

Ƴancin kai: An tsaurara tsaro a Kano

"Dangane da bikin ranar ‘yancin kai mai zuwa ranar 1 ga Oktoba, 2024, rundunar ‘yan sanda ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace don samar da tsaro.
"Saboda haka muna kira ga mutanen Kano su ba ƴan sanda da sauran jami'an tsaro haɗin kai wajen gudanar da shagalin wannan rana, su bi dokokin da aka shinfiɗa.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Kungiyoyin Arewa sun amsa kiran fitowa tituna a ranar 1 ga Oktoba

"Haka nan an tura dakarun tsaro zuwa wasu muhimman wurare a cikin jihar Kano domin dakile duk wata barazana tsaro daga masu zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba."

- SP Abdullahi Kiyawa.

Zanga-zanga ta gamu da cikas a Kaduna

A wani rahoton kuma zanga-zangar da ake shirin yi ranar 1 ga watan Oktoba ta gamu da cikas, wata ƙungiya ta roki ƴan Kaduna su canza tunani.

Mai magana da yawun ƙungiyar CCC reshen Kaduna, Kwamared Yusuf Lawal ya ce zanga-zangar ba ta da amfani duba da abin da ya faru a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262