1 Oktoba: Rundunar Yan Sanda Ta Kara Yawan Jami'ai a Arewacin Najeriya

1 Oktoba: Rundunar Yan Sanda Ta Kara Yawan Jami'ai a Arewacin Najeriya

  • Rundunar yan sandan kasar nan reshen jihar Yobe ta bayyana cewa akwai shiri na musamman kan ranar 1 Oktoba
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Garba Ahmed ne ya bayyana haka, inda ya ce an an kara yawan jami'an tsaro a fadin jihar
  • Rundunar ta nemi hadin kan shugabannin gargajiya da kungiyoyi masu zaman kansu wajen tabbatar da zamansu lafiya a Yobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Rundunar yan sandan Yobe ta kara yawan jami'an tsaro a fadin jihar domin tabbatar da tsaro yayin bikin zagayowar ranar samun yancin kan kasar nan.

Najeriya za ta cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka, sai dao gwamnatin tarayya ta ce a yi bikin saffa-saffa saboda matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

Kaduna: An zargi sojoji da sake jefa bama bamai a masallaci aka kashe bayin Allah

Police
Yan sanda sun kara yawan jami'an tsaro a Yobe Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kwamishinan yan sandan jihar, Garba Ahmed ya ce jami'ansu za su tabbata an yi bikin cikin lumana a jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun tsaurara tsaro gabanin Oktoba

Jaridar Independent Newspaper ta tattaro cewa kakakin rundunar yan sandan Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya ce an girke jami'a a wurare daban-daban a jihar.

Ya ce an samar da yan sandan domin tsaron rayuka da dukiyoyin jama'ar Yobe yayin da ake bikin samun yancin kan kasar nan.

Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a

Rundunar yan sandan jihar Yobe ta nemi hadin kan shugabanni, kungiyoyin siyasa da sauran jama'ar gari wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a gobe.

An kuma bukaci mazauna jihar su tabbata sun sanya idanu kan shige da fice, musamman idan aka yi la'akari da yadda zanga-zanga ta juye zuwa rikici a baya.

Kara karanta wannan

Zanga zangar Oktoba: Yan sanda sun yi zazzafan shiri a jihohin Arewa da Kudu

Yan sandan Yobe sun kama basarake

A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sandan Yobe ta kama wani dagaci, Magajin Garin Gazarkuma da ke ƙaramar hukumar Nangere bisa zargin hannu a kisan direban motar tarakta.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da kama Magajin Garin bayan ya ja zugar matasa inda su ka kai hari gonar Maigari Mato a kauyen Gubate.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.