‘Ka Yi Hankali,’ Dattawan Arewa Sun Gargadi Tinubu kan Korar Ministoci
- Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan maganar sauya ministoci da zai yi
- Kungiyar ta ce akwai ministocin da suka nuna zalaƙa a karkashin mulkin Bola Tinubu da bai kamata a sauya su ba kwata kwata
- A makon da ya wuce ne gwamnatin tarayya ta sanar da shugaban kasa Tinubu zai yi sauye sauye a cikin majalisar zartarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata kungiyar dattawan Arewa maso yammacin Najeriya ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar ta ce ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi taka tsan-tsan wajen yunkurin sauya wasu ministoci.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Dakta Adamu Giwa ne ya yi kiran ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gargadi Tinubu kan korar ministoci 3
1. Ministan gidaje
Wata kungiyar dattawan Arewa maso Yammacin Najeriya ta ce ministan harkokin gidaje, Ahmad Dangiwa ya yi kokari sosai.
Kungiyar ta kafa dalilin cewa ministan ya kawo tsare-tsaren da suka kawo sauyi wajen samar da gidaje ga ma'aikata.
2. Ministan kasafin kudi
The Guardian ta wallafa cewa ƙungiyar ta ce ministan tsare-tsare da kasafin kudi, Abubakar Atiku Bagudu ya nuna zalaƙa sosai.
A cewar kungiyar, Atiku Bagudu ya nuna kwarewa wajen fito da tsare-tsaren da suka sanya gwamnati kashe kudi a kan ƙa'ida.
3. Ministan tsaro
Kungiyar ta ce karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya nuna bajinta wajen jawo kashe manyan jiga jigan yan bindiga a Arewa.
Saboda haka shugaban kungiyar ya ce ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sakayya mai kyau ne ga ministocin ba wai korar su ba.
Tinubu ya ci bashin $1.57bn
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara kinkimo bashin $1.57bn daga bankin duniya domin ayyuka na musamman.
An ruwaito cewa Bankin Duniya ya amince da ba gwamnatin tarayya bashin ne domin yin ayyuka na musamman guda uku a fadin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng