Oktoba: An Fadawa Tinubu Sirrin Shawo kan Matasa Masu Shirin Zanga Zanga
- Kungiyoyin fararen hula sun yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zangar Oktoba
- Shugabannin kungiyoyin sun ce har yanzu shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai makara ba wajen shawo kan matasan Najeriya
- A gobe Talata, 1 ga watan Oktoba matasan Najeriya za su fito kan tituna domin nuna adawa da tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da shirin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ke kara daukan ɗumi an kawo mafita ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Wasu kungiyoyin fararen hula sun ce har yanzu shugaba Bola Tinubu zai iya shawo kan matasan Najeriya.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa kungiyoyin sun ce tsare wasu masu zanga zanga na cikin abin da ya kara tunzura matasan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hanyar shawo kan masu zanga zanga
Wasu kungiyoyin fararen hula da Auwal Musa Rafsanjani ke jagoranta sun bukaci Bola Tinubu ya gaggauta tattaunawa da matasan Najeriya.
Auwal Musa Rafsanjani ya ce za a iya dakile yunkurin zanga zangar Oktoba idan gwamnati ta nemi matasa domin tattaunawa.
Tinubu bai kyauta ba inji Rafsanjani
Auwal Musa Rafsanjani ya ce Bola Tinubu bai nuna halin dattaku ba wajen rashin tattaunawa da matasa bayan zanga zangar Agusta.
Rafsanjani ya ce a lokacin zanga zangar shugaban kasa ya yi kira kan tattaunawa da matasan amma daga baya zancen ya wuce a haka.
Kiran Rafsanjani ga masu zanga zanga
Shugaban kungiyoyin ya yi tir ga matasan Najeriya wajen yin zanga zanga lami lafiya idan gwamnatin tarayya ba ta neme su ba.
Rafsanjani ya ce akwai bukatar su nisanci sace sace, fashe fashe da duk wani nau'in tayar da tarzoma a yayin zanga zangar.
An saka lokutan zanga zanga a jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar 1 ga Oktoba matasan Najeriya suka ce za su fito zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a mulkin Bola Tinubu.
Yayin da ake saura kwana ɗaya da fara zanga zangar, matasa sun sanar da wurare da lokutan da za su fito a garuruwan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng