Ranar Ƴanci: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ƙara Ba Ƴan Najeriya Hakuri, Ya Yi Masu Albishir
- Sanata Godswill Akpabio ya ƙara bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki na ƙunci da yunwa a faɗin ƙasar
- Shugaban majalisar dattawa ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan komai zai wuce kuma mutane za su shiga cikin walwala
- Akpabio ya bayyana haka ne a wurin taron da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 64 da samun ƴanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya roki ƴan Najeriya su ƙara haƙuri tare da yi wa ƙasarsu kyakkyawan fata.
Sanata Akpabio ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa lokacin farin ciki da walwala na nan tafe ba da jimawa ba, don haka ya roki a ƙara hakuri.
Daily Trust ta ce Akpabio ya faɗi haka ne a wani taro da aka shirya a babbar cocin ƙasa da ke Abuja a wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Akpabio ya ƙara bada haƙuri
Ya aminta da wahalar da al'umma ke ciki amma duk da haka ya roƙi mutane su haɗa kai wajen gina ƙasar nan ta yadda goben yara da matasa za ta yi kyau.
"Duk da muna murnar wannan rana ba za mu manta da halin ƙunci da tsadar rayuwa da ake ciki ba, tabbas muna cikin wani yanayi amma idan muka haɗa kai komai zai wuce.
"Aikin da muka tattago na ceto ƙasar nan yanzu aka fara amma ina rokon ku kada ku sare, ku ƙara hakuri kuma ka da ku cire rai, babu makawa za mu ga canji."
"Haske na nan tafe, idan muka dunƙule wuri ɗaya za mu gina ƙasar nan ta yadda 'ya'yanmu da jikoki masu zuwa za su yi alfahari da ita."
- Godwill Akpabio.
"An san ƴan Najeriya da juriya" - Akpabio
Ya kuma bayyana irin halin da ‘yan Najeriya ke da shi na jurewa da kuma shawo kan kalubale masu tarin yawa tun daga fafutukar neman ‘yancin kai na farko zuwa yau.
Shugaban majalisar dattawan ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ya dage tare da jan ragamar Najeriya zuwa matakin ci gaba, rahoton This Day.
Atiku Bagudu ya kare manufofin Tinubu
A wani rahoton kuma ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu ta bayyana cewa cire tallafin fetur zai amfani kasar nan.
Atiku Bagudu, wanda tsohon gwamnan Kebbi ne ya ce shugaba Bola Tinubu ya damu matuka da halin da kasa ke ciki kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng