Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Barazanar ASUU da Gaske, Ta Fara Daukar Mataki
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma'aikatar ilmi ta fara shirin ganin ta hana ASUU shiga yajin aiki a ƙasar nan
- Ma'aikatar ilmin ta samar da tawaga da za ta yi aiki domin ganin cewa ƙungiyar ASUU ba ta fara yajin aikin ba
- Hakan na zuwa ne dai bayan ASUU ta ba gwamnati wa'adin kwanaki 14 ta warware matsalolin da ke tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar ilmi ta fara ƙoƙarin ganin ta hana ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) shiga yajin aiki.
Ma'aikatar ilmin ta bayyana cewa tana aiki domin ganin cewa ƙungiyar ASUU ba ta shiga yajin aikin da ta yi barazanar farawa ba.
Wane mataki gwamnati ta ɗauka?
Jaridar The Punch ta ce daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar ilmi ta tarayya, Folasade Biriowo, ya shaida mata hakan yayin wata tattaunawa a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman ya samar da wata tawaga wacce ke aiki domin ganin ba a shiga yajin aikin ba.
"Ina ba da tabbacin cewa ana yin duk mai yiwuwa domin gani an hana aukuwar yajin aikin. Tuni minista ya samar da tawagar da ke aiki a kan hakan. Ina ba da wannan tabbacin."
- Folasade Biriowo
ASUU ta ba gwamnati wa'adi
A makon da ya gabata ne ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ta warware dukkanin matsalolin da ke tsakaninsu, sannan idan ba ta yi hakan ba za ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban ƙungigar ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnati take tafiyar hawainiya wajen aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimmawa.
Ya bayyana cewa hakan da gwamnatin ke yi na ƙara taɓarɓarar da al'amura a jami'o'i mallakar gwamnati.
ASUU ta tsunduma yajin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) reshen jami'ar jihar Gombe ta sanar da fara yajin aiki.
A yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024 ne ƙungiyar ta shiga yajin aikin bayan gwamnatin jihar Gombe ta gaza biya mata buƙatun da take nema.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng