Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Kare Tinubu, Ya Ba 'Yan Najeriya Shawara

Tsadar Rayuwa: Jigon APC Ya Kare Tinubu, Ya Ba 'Yan Najeriya Shawara

  • Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya fito ya kare shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan halin da tattalin ƙasar nan ke ciki
  • Olatunbosun Oyintiloye ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara ba Tinubu lokaci domin ya warware matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta
  • Ya bayyana cewa shugaban ƙasan yana aiki tuƙuru domin ganin ya dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan kan turba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya yi magana kan salon mulkin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jigon na APC ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara ba shugaba Tinubu lokaci domin shawo kan matsalar tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fuskanta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban NURTW da wasu mutum 3 a Kaduna

Jigon APC ya goyi bayan Tinubu
Jigon APC ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce jigon na APC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi, a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara ya ba ƴan Najeriya?

Olatunbosun Oyintiloye ya ce ana ƙara haƙuri kaɗan, dukkanin ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta za su zama tarihi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Oyintiloye, wanda ya amince da cewa ƴan Najeriya na cikin mawuyacin hali, ya ce shugaban ƙasan ba ya barci a kan hakan, sannan yana aiki dare da rana domin gyara tattalin arzikin ƙasar nan.

'Dan siyasar ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su tuna cewa ba Shugaba Tinubu ba ne ya samar da matsalar tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fama da shi ba.

Jigon APC ya kare Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram

Sai dai, ya ce duk da manufofin tattalin arziƙin da shugaban ƙasar ke aiwatarwa na iya zama masu tsauri, amma an kawo su ne domin ɗora ƙasar nan a kan turbar da tattalin arziƙinta zai bunƙasa.

Oyintiloye ya bayyana cewa, Tinubu ya hau karagar mulki ne a lokacin da tattalin arziƙin ƙasar nan ya durƙushe, wanda hakan ya sa ye buƙatar gyara da fahimtar ƴan Najeriya.

Ya ce yayin da shugaban ƙasa ke ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan sannu a hankali, yana buƙatar haƙuri, addu’a, da goyon bayan duk ƴan Najeriya domin abubuwa su daidaita.

Tinubu ya yi naɗe-naɗen mukamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa majalisar gudanarwa ta farko a sabuwar hukumar raya shiyyar Arewa maso Yamma (NWDC).

Shugaban ƙasar ya aika sunayen mutum tara da ya naɗa a hukumar ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng