Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyen Ministan Tsaro, Sun Sace 40 da Hallaka Wasu

Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyen Ministan Tsaro, Sun Sace 40 da Hallaka Wasu

Yayin da ake cin galaba kan kan bindiga, miyagu sun sake kai hari a jihar Zamfara inda suka hallaka mutane biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Wasu yan bindiga sun kai wani hari a jihar Zamfara inda suka sace mutane da dama.

Maharan sun sace akalla mutane 40 tare da hallaka wasu guda biyu a Janboka da ke karamar hukumar Maradun.

Yan bindiga sun kai hari kauyen Matawalle inda suka hallaka mutane
Yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara tare da sace mutane 40 da hallaka mutane 2. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Zamfara: Yan bindiga sun kai sabon hari

Premium Times ta ruwaito cewa daga cikin wadanda yan bindigan suka sace akwai yara da kuma mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maradun nan ne garin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wanda shi ne tsohon gwamnan jihar da ya sauka.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya yi ajalin mace mai shayarwa da wasu mutane 3 a Zamfara

Lamarin ya faru ne a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 yayin da aka jibge dakarun sojoji a yankin Arewa maso Yamma domin yakar yan bindiga.

An bayyana mutane 2 da aka hallaka

Wani mazaunin yankin, Ibrahim Haru ya ce yan bindigan sun shigo kauyen ne inda suka rika yin harbi ta ko ina.

Haru ya ce mafi yawan wadanda aka sace mata ne da yara inda ya ce washegari da safiyar Lahadi an irga fiye da mutane 40 da aka sace.

Ya ce daga cikin wadanda aka hallakan akwai wani Malam Isha da kuma matashi yayin da suke shirin guduwa.

Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan yan bindiga sun sake mutane 10 da suka yi garkuwa da su.

Maharan sun sake su ne bayan karbar kudin fansa har N10m daga iyalansu kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Gwamna Dauda ya yi magana kan yan bindiga

Kara karanta wannan

Yadda NNPCL ya gano satar mai har zuwa masallatai da coci, ya dauki mataki

Kun ji cewa Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ba zai yi sulhu da ƴan bindiga masu kashe mutane ba a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare kan maɓoyar ƴan bindigan.

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi na yaƙi da ƴan ta'adɗa waɗanda suka addabi jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.