Gwamna Ya Fadi Yadda Cire Tallafi Ya Ceto Najeriya, Ya ba Matasa Shawara

Gwamna Ya Fadi Yadda Cire Tallafi Ya Ceto Najeriya, Ya ba Matasa Shawara

  • Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana amfanin cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi a Najeriya
  • Abiodun ya ce cire tallafin zai taimaka wurin habaka tattalin arziki wanda zai shafi dukan bangarorin kasar
  • Gwamnan ya ce matakin da Tinubu ya dauka ya ceto Najeriya tare da samun rarar N5.4bn na kudi ga kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya yabawa

Gwamna kan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Abiodun ya ce cire tallafin ya taimaka an samu rarar makudan kudi har N5.4bn saboda matakin.

Gwamna ya yabawa Tinubu kan cire tallafin mai a Najeriya
Gwamna Dapo Abiodun ya fadi amfanin cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi. Hoto: Gov. Dapo Abiodun.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

'Wahala za ta kare', Minista ya fadi yadda Tinubu ke kokarin dakile halin kunci

Gwamna ya yabi Tinubu kan cire tallafi

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taro a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun a yau Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024, cewar Punch.

Abiodun ya ce matakin cire tallafin zai kawo sauyi a Najeriya musamman ta bangaren tattalin arziki.

"Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dauki mataki mai tsauri wanda ba kowa ba ne zai iya."
"Matakin zai taimaka wurin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durkushewa saboda wasu tsare-tsaren baya."
"Dole mu yi hakuri mu kuma gane cewa cire tallafin ya rage yawan kudi da ake kashewa har N5.4bn."

- Dapo Abiodun

Gwamna Abiodun ya shawarci matasa

Abiodun ya ce raran da aka samu har na N5.4bn zai taimaka wurin kaddamar da manyan ayyuka da inganta rayuwar al'umma.

Ya ce zanga-zangar da ake shirin fita babu abin za ta kawo sai yawan sace-sace da barnata dukiyoyin al'umma, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

Har ila yau, gwamnan ya bukaci yan Najeriya su dage da addu'a inda ya ce gwamnatin Tinubu ta himmatu wurin tafiya da kowa.

Cire tallafi: Dogara ya kare Tinubu

Kun ji cewa Tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa babau laifin shugaba Bola Tinubu a cire tallafin mai Rt. Hon.

Dogara ya ce tun kafin hawan Tinubu mulki aka cire tallafin mai a Najeriya kawai shi ya tabbatar da haka ne a baki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.