Yadda NNPCL Ya Gano Satar Mai Har Zuwa Masallatai da Coci, Ya Dauki Mataki
- Kamfanin mai na NNPCL ya bayyana yawan asara da yake yi musamman saboda satar mai da ake yi a Najeriya
- Kamfanin ya koka kan yadda ya bankado yawan sace-sacen tare da gano wasu bututun mai zuwa wuraren ibada
- Jami'in yada labarai a kamfanin, Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa an lalata matatun mai ba bisa ka'ida kusan 8,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPCL ya yi magana kan yawan satar man da ake yi yanzu a Najeriya.
Kamfanin ya nuna damuwa kan yadda ya gano sabon salo na satar mai din har wuraren ibada da masarautu.
NNPCL ta koka kan yawan satar mai
Jami'in sadarwa na kamfanin, Olufemi Soneye shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soneye ya ce tabbas a yanzu satar ta yi yawa wanda har wuraren ibada sun gano bututun mai da ake amfani da su.
Ya ce kamfanin ya samu nasarar kara samar da mai daga ganga miliyan 1.7 zuwa ganga miliyan uku inda ya ce babban cigaba ne.
Yawan matatun mai da aka lalata
Mataimakin manaja a sashen kula da harkokin kamfanin NNPCL, Murtala Mohammed a bangarensa ya bayyana yadda ake satar a bayyane.
Mohammed ya ce akalla matatatun mai 8,000 ne aka lalata wadanda aka samar da su da yawa ba bisa ka'ida ba.
Jami'in ya ce an lalata matatun ne da aka samar ba bisa ka'ida ba a cikin watanni shida kacal da suka gabata.
Tinubu ya magantu kan rigimar Dangote, NNPCL
Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana kan rigimar da ke faruwa tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote.
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ba zai tsoma baki kan rigimar da ke faruwa tsakaninsu ba saboda suna cin gashin kansu.
Wannan na zuwa ne yayin da aka fara takun-saka tsakanin kamfanonin guda biyu tun bayan Dangote ya fara fitar da mai.
Asali: Legit.ng