Gwamna Abba Ya Yi Ta'aziyyar 'Yan Sandan da Suka Rasu, Ya Tuna da Iyalansu
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ta'aziyya kan rasuwar jami'an ƴan sanda guda biyar sakamakon hatsarin motan da ya ritsa da su
- Gwamna Abba ya yi addu'ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma ba waɗanda suka jikkata lafiya
- Gwamnan ya kuma ba da N500,000 ga iyalan kowane daga cikin jami'an da suka rasu sakamakon hatsarin motar da ya auku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa iyalan jami’an ƴan sanda biyar da suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Karfi da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria.
Hatsarin motan ya auku ne a ranar Talatar da ta gabata yayin da suke dawowa daga jihar Edo bayan an kammala zaɓen gwamnan jihar.
Saƙon ta’aziyyar gwamnan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya yi ta'aziyya a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati, sun ziyarci rundunar ƴan sandan yankin Bichi domin jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata a hatsarin.
"A madadin gwamnati da kuma al’ummar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya sa Aljannah ta zama makoma ga waɗanda suka rasu, Ya kuma ba waɗanda suka jikkata lafiya, Ya kuma kare aukuwar irin hakan a gaba."
"Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma bayar da gudummawar Naira 500,000 ga iyalan kowane daga cikin jami’an da suka rasu da kuma N250,000 ga kowane jami’i daga cikin jami'an da suka jikkata."
- Sanusi Bature Dawakin Tofa
Gwamna Abba ya yi ƙoƙari
Ibrahim Zulkiful ya yaba da ziyarar ta'aziyyar da gwamnan ya kai ga iyalan ƴan sandan da suka rasa ransu sakamakon hatsarin motan.
Sai dai, ya bayyana cewa ya kamata a ce abin da gwamnan ya ba su ya fi N500,000 duba da halin da ake ciki.
"Eh gaskiya gwamnan ya yi musu ƙauro, ya kamata a ce abin da ya ba su yafi hakan sosai."
- Ibrahim Zulkiful
Ƴan sandan Kano sun rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta komawa Kano daga jihar Edo.
Rahotanni sun ce hatsarin motar ya rutsa da akalla jami'an ƴan sandan Kano 15 inda biyar suka mutu yayin da sauran 10 suka jikkata.
Asali: Legit.ng