Sanata Ya Cigaba da Tonon Silili, Ya Fallasa Rashin Gaskiyar ‘Yan Siyasar Kasar nan
- Ali Muhammad Ndume ya na ganin an tara barayi da marasa gaskiya a cikin masu rike da mukamai a yau
- Sanatan na Kudancin jihar Borno ya ce mafi yawan ‘yan siyasa da wadanda ke kujerun gwamnati barayi ne
- Wadanda suka kubuta daga wannan danyen aiki su ne wasu kilan da Ndume ya ce su na da tsoron Ubangiji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Muhammad Ndume, ya sake ragargazar abokan aikinsa a siyasa.
Sanata Ali Muhammad Ndume ya koka game da yadda rashin gaskiya ta yi kamari a kasar nan, yake cewa abin ya zama babbar matsala.
''Yan siyasa ba gaskiya' - Sanata Ndume
Ranar Asabar jaridar premium Times ta rahoto ‘dan majalisar ya na cewa rashin gaskiya yana cikin kalubalen da ke addabar kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da wasu manema labarai jiya a Kano.
Akwai dokokin cafke barayin 'yan siyasa?
Ali Muhammad Ndume yake cewa har yau babu wata doka da ake da ita wanda za ta yaki sata da rashin gaskiya da ake yi a Najeriya.
Ndume wanda aka dakatar a majalisar dattawa a baya ya ce a Najeriya ne kurum mutum zai sace dukiyar jama'a, kuma a yaba masa.
“Idan ku ka ga wani a cikin tsarinmu, musamman a siyasa ko a gwamnati, kuma bai da rashin gaskiya, to ya yi sa’a cewa ya na da tsoron Allah.
"A kasar nan ne kurum mutum bai da kudi jiya ko a makon jiya, amma a mako mai zuwa zai saye motoci 10, jirgin sama, kuma danginsa su rika alfahari da shi".
- Sen. Muhammad Ali Ndume
Yunkurin Sanata Ndume bai je ko ina ba
A wasu kasashe, Daily Trust ta rahoto Sanatan ya na cewa idan mutum ya yi kudi a dare daya, za a nemi a ji yadda ya samu dukiyar ne.
Ndume ya ce ya yi ta kokari wajen kawo dokar da za ta sa a rika kama wadanda ake zargi da satar dukiyar al’umma, amma bai dace ba.
Ubangiji ya yi wa Najeriya arziki, amma talakawa ba su iya mora a cewar ‘dan majalisar.
Rashin gaskiyar 'yan kasuwa
Abin bai tsaya a siyasa ba, an rahoto Abdul Samad Rabiu ya ce akwai hannun mugayen 'yan kasuwan wajen tsadar kaya.
Mai kudin ya fadi yadda ‘yan kasuwa su ke sa farashi ya tashi duk da kokarin kamfanin BUA na yi wa al'umma rangwame.
Asali: Legit.ng