Rai Baƙon Duniya: Mahaifiyar Tsohon Gwamna a Arewa Ta Kwanta Dama
- Tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ya tafka babban rashi bayan mutuwar mahaifiyarsa a jiya Asabar
- Marigayiyar, Mama Jummai Eli Nyame Kala ta rasu ne cikin salama a daren jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024
- Sakataren yada labaran tsohon gwamnan, Hon. Obidah Bitrus shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar mai suna Jumai Eli Nyame ta rasu ne a daren jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.
Mahaifiyar tsohon gwamnan Taraba, Nyame ta rasu
Leadership ta ruwaito cewa sakataren yada labaran tsohon gwamnan, Hon. Obidah Bitrus shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bitrus ya ce dattijuwar ta rasu ne cikin salama da misalin karfe 10.00 na daren ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.
"Cikin alhini mu ke sanar da rasuwar uwa kuma kaka a gare mu mai suna Mama Jummai Eli Nyame Kala."
"Mama, ita ce mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da ya yi mulki jihar har wa'adi uku."
"Ta rasu a daren ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 da misalin karfe 10.00 cikin salama."
- Hon. Obidah Bitrus
Gudunmawar da marigayiyar ta bayar a rayuwarta
Bitrus ya bayyana irin gudunmawar da dattijuwar ta bayar wurin inganta rayuwar al'umma da dama yayin da take raye.
Ya ce tabbas za a yi rashin Mama kuma ba za a taba mantawa da ita saboda taba rayuwar mutane da ta yi.
Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan Taraba
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya, Architect Darius Ishaku.
Hukumar yaki da cin hanci ta cafke Ishaku kan zargin badakalar makudan kudi har N27bn a ranar Juma'a 27 ga watan Satumbar 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama tsohon gwamnan ne a gidansa da ke birnin Abuja a daren ranar Juma'a kan zargin laifuffuka 15.
Asali: Legit.ng