Hada Baki da 'Yan Bindiga: Hukumar NSCDC Ta Dauki Mataki kan Jami'inta
- Hukumar NSCDC ta yi Allah wadai kan jami'inta wanda aka cafke bisa laifin safarar makamai da ƙwayoyi ga ƴan bindiga a jihar Zamfara
- Kwamandan NSCDC na jihar Zamfara ya bayyana cewa hukumar ta ɗauki matakin kora da tuhuma a kan jami'in da aka cafke bisa aikata laifin
- Sani Mustapha ya sha alwashin cewa hukumar za ta tabbatar da cewa jami'in ya fuskanci fushin hukuma saboda wannan mummunan aikin da ya aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Hukumar NSCDC a jihar Zamfara ta sha alwashin hukunta jami'inta da aka samu da laifin safarar makamai da ƙwayoyi ga ƴan bindiga.
Hukumar NSCDC ta kori jami'in mai suna Maikano Sarkin-Tasha wanda ƴan sanda suka cafke.
Kwamandan NSCDC na jihar Zamfara, Sani Mustapha ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a hedkwatar hukumar da ke birnin Gusau, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NSCDC za ta hukunta jami'inta a Zamfara
Sani Mustapha ya yi Allah wadai da wannan mummunar ɗabi'ar da jami'in ya nuna, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
"Mun yi Allah wadai da wannan aikin ta kowace fuska domin hukumarmu an santa da gaskiya wajen gudanar da ayyukanta, ɗa'a da bin ƙa'idojin aiki."
"Hukumar ba ta lamuntar rashin ɗa'a, cin hanci da rashawa, aikata laifi ko wani mummunan abu da bai kamata jami'i ya yi ba."
- Sani Mustapha
Kwamandan na NSCDC ya bayyana cewa zai tattauna da kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Dalijan, domin ɗaukar mataki na gaba.
Ya ba da tabbacin cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa, bincike da tuhuma da tabbatar da cewa jami'in ya fuskanci fushin hukuma.
NSCDC ta bankaɗo shirin ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan hukumar tsaron farar hula (NSCDC), Dakta Abubakar Ahmed Audi ya ce za a tura jami'an hukumar 30,000 zuwa sassan Najeriya.
CG Abubakar Audi ya ce za a tura jami'an ne domin ba da kariya ga kadarorin kasa a yayin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa a faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng