Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram

Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram

  • Dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Sojojin sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kai hari da ƴan ta'addan suka yi a kan titin hanyar Magumeri-Maiduguri a jihar
  • Jajirtattun jami'an tsaron bayan sun fatattaki ƴan ta'addan sun kuma ƙwato tarin makamai masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar MNJTF na Operation Hadin Kai, sashi na uku, sun daƙile wani yunƙurin kai hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a Borno.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun yi yunƙurin kai harin ne a titin hanyar Magumeri-Maiduguri a Borno.

Sojoji sun murkushe 'yan Boko Haram
Dakarun sojoji sun dakile harin 'yan ta'addan Boko Haram Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato tarin makamai da alburusai daga hannun ƴan ta’addan, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ya ajiye makamai, ya miƙa wuya ga rundunar sojoji a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yaɗa labaran MNJTF, Laftanar Kanal Olaniyi Osaba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Maiduguri, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Yadda sojoji suka daƙile harin Boko Haram

Ya bayyana cewa sojojin sun yiwa ƴan ta'addan kwanton ɓauna inda suka murƙushe su kafin su kaiwa fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba hari.

Laftanar Kanal Olaniyi Osaba ya yi bayanin cewa sojojin sun yi lamɓo ne a kan hanyar ƴan ta'addan sannan suka buɗe musu wuta bayan sun fito daga daji a kan babura.

"Bayan sun hango dakarun sojojin, ƴan ta'addan sun yi ƙoƙarin guduwa amma sai sojojin suka buɗe musu wuta."
"Wannan buɗe musu wutan da suka yi ya tilasta ƴan ta'addan suka bar makamansu da baburansu, wanda hakan ya rusa shirinsu na kai hari a yankin."

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Masu shirya sabuwar zanga zanga sun aika saƙo ga ƴan sandan Najeriya

- Laftanar Kanal Olaniyi Osaba

Olaniyi Osaba ya lissafo makaman da aka ƙwato a hannun ƴan ta'addan da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, alburusai guda 51 masu kaurin 7.62mm, jigida guda biyu, alburusai guda 61, ƙunshin tabar wiwi, Tiramol da sauran abubuwa.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 1,937 a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumban 2024.

DHQ ta ƙara da cewa an cafke mutane 2,782 da ake zargi tare da ceto wasu mutane 1,854 da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng