Garambawul: Tinubu Zai Sallami Ministoci 11 da Wani babban Jami'in Gwamati

Garambawul: Tinubu Zai Sallami Ministoci 11 da Wani babban Jami'in Gwamati

  • Ana sa ran garambawul da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi a majalisar ministocinsa zai kasance bisa kwararan hujjoji
  • An yi ta kiraye-kiraye na cewa Shugaba Tinubu ya tsige wasu daga cikin ministocinsa saboda gaza tabuka abin kirki a gwamnatance
  • Wani sabon rahoto ya bayyana cewa garambawul din da zai shafi ministoci kusan 11 da kuma wani babban jami'in gwamnatin tarayyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Yayin da ake ci gaba da dakon sanarwar garambawul da Shugaba Bola Tinubu ya ce zai yi a majalisar ministocinsa, an ce mutane da dama za su rasa mukamansu.

An ce za a mayar da wasu ministocin zuwa wasu ma'aikatun yayin da za a kori wadanda aka amince cewa ba su iya tabuka komai ba daga lokacin da aka nada su zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin shiyya: An samu baraka tsakanin sanatoci kan bitar kundin tsarin mulki

Rahoto ya gano ministocin Tinubu da za su iya rasa kujerunsu a garambawul
Garambawul: Ana sa ran Tinubu zai kori ministoci 11 da wani jami'in gwamnati. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Garambawul a majalisar ministoci

Wasu ministocin da ke fargabar za a tsige su daga majalisar ministocin sun fara kamun kafa tare da iyayen gidansu domin dakile hakan daga faruwa, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon yadda lamura ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan ya sa masu ruwa da tsaki ke nuna muhimmancin yin garambawul a majalisar ministocin cikin gaggawa.

Kamar yadda rahoton jaridar na ranar Alhamis, 26 ga Satumba ya nuna, ministoci 11 (daga cikin sama da 40) ne aka rubuta sunayensu a cikin wadanda za a tsige.

Ministocin da suka gaza cin maki

Rahoton ya ce za a tsige Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Tinubu, kuma da yiwuwar a maye gurbinsa da tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola.

An ce Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin yiwa haraji da kasafi garambawul ne zai zama karamin ministan Wale Edun na ma'aikatar kudi da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

Rahoton jaridar ya ambato wasu majiyoyi na cewa Tinubu zai dawo da wani minista da ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari.

An kuma rahoto cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ministan ayyuka, David Umahi da ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ba su tsallake makin da ake so ba.

Tinubu zai kori Gbajabiamila

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai sallami Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadarsa saboda gaza tabuka abin kirki a aikinsa.

Majiyoyi sun shaida cewa Gbajabiamila na daga cikin wadanda za su iya rasa aikinsu a garambawul din da Tinubu zai yiwa ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.