Rigima Ta Barke da Dattawa Suka Kalubalanci Gwamna kan Nadin Sabon Sarki

Rigima Ta Barke da Dattawa Suka Kalubalanci Gwamna kan Nadin Sabon Sarki

  • Zanga-zanga ta barke yayin da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya tabbatar da nadin sabon sarki
  • Dattawa da shugabannin yankin Okpella a jihar sun yi fatali na nadin Lukman Akemokhue a matsayin sarki
  • Gwamnan ya tabbatar da nadin tare da mika takardar mukamin a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - An samu tashin hankali a yankin Okpella da ke jihar Edo kan rigimar sarauta.

Dattawa da kuma shugabannin yankin sun kalubalanci matakin Gwamna Godwin Obaseki na nadin basarake.

An kalubalanci gwamnan PDP kan nadin sarauta ba bisa ka'ida ba
Dattawa sun yi fatali da nadin sarauta da Gwamna Godwin Obaseki ya yi a Edo. Hoto: Gov. Godwin Obaseki.
Asali: Twitter

Sarauta: Dattawa sun kalubalanci Obaseki

Punch ta ruwaito cewa rigimar ta fara ne bayan Gwamna Obaseki ya nada Lukman Akemokhue a matsayin sarkin Okpella.

Kara karanta wannan

Rigima ta yi kamari da Gwamna ya zargi mataimakinsa da shirin kutse a gidan gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obaseki ya tabbatar da nadin ne a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 inda ya ci karo da matsaloli.

Sai dai dattawa da shugabannin yankin sun yi fatali da nadin inda suka ce an saba ka'idar al'adunsu na nadin sarauta, cewar rahoton The Guardian.

Zanga-zangar ta barke ne kwana daya bayan mika takardar nadin sarautar a ma'aikatar kananan hukumomi da ke brnin Benin City da ke jihar.

An zargi Obaseki da kakaba sabon sarki

Wani shugaban yankin mai suna Abu Abdulganiyu da ya jagoranci zanga-zangar ya zargi Obaseki da kakaba musu basarake.

"Wannan mataki ya saba ka'idar nadin sarauta a al'adarmu saboda ba sarauta ce ta siyasa ba."
"Dole ne a kare martabar kujerar, mu na da sarki, mun san wanda mu ke so, Obaseki ba zai kakaba mana ba saura makwanni ya bar ofis."

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Sarakuna sun roki Tinubu alfarma game da Yahaya Bello

- Abu Abdulganiyu

Obaseki ya shiga kafar wanda da Shaibu

Kun ji cewa mako daya bayan kammala zaben gwamnan Edo, gwamnatin jihar ta zargi mataimakin gwamna, Philip Shaibu da neman rigima.

Gwamnatin jihar ta zargi Shaibu ta shirya makarkashiya domin mamayar gidan gwamnati a ranar Litinin 30 ga watan Satumbar 2024.

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta tabbatar da Shaibu a matsayin halastaccen mataimakin gwamnan jihar bayan tsige shi da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.