Rashin Tsaro: Gwamna Dauda Ya Fadi Matsayarsa kan Sulhu da 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: Gwamna Dauda Ya Fadi Matsayarsa kan Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ba zai yi sulhu da ƴan bindiga masu kashe mutane ba a jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare kan maɓoyar ƴan bindigan
  • Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin da take yi na yaƙi da ƴan ta'adɗa waɗanda suka addabi jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi la'akari da kiran da ƴan ta'adda suka yi na dakatar da kai harin bam a maɓoyarsu ba.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da sojojin saman Najeriya suka yi na ci gaba da kai hare-hare kan ƴan bindiga da ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma, musamman Zamfara har sai an samu zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

"Na fi ƙarfinku," Ministan Tinubu ya ƙara ta da Hazo, ya yiwa wasu gwamnoni shaguɓe

Gwamna Dauda ya magantu kan 'yan bindiga
Gwamna Dauda ya ce ba maganar sulhu da 'yan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarinta na yaƙi da ƴan ta'adda, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da miyagu ba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Dauda ya ce kan ƴan bindiga?

Gwamna Dauda wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yaɗa labaran sa, Sulaiman Idris, ya yi kira ga ƴan bindiga da sauran ƴan ta’adda a jihar da su ajiye makamansu.

"Ba a yin sulhu da masu kisan kai yayin da suke riƙe da muggan makamai. Ya kamata su fara miƙa kansu ga hukuma, sannan mu auna matakin ɗauka na gaba."
"A halin yanzu, ba mu ga wata nadama daga ƴan bindigan ba. An kashe akasarin shugabanninsu da sauran ƴan bindiga a a atisayen ‘Ceton Arewa’ wanda aka fara makonnin da suka gabata. Za a ci gaba da kai musu hare-hare har sai sun miƙa wuya."

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan matsalar tsaro, ya ba da shawara

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya yi daidai

Jamilu Musa ya shaidawa Legit Hausa cewa matakin gwamnan na ƙin yin sulhu da ƴan bindiga abin a yaba ne.

Ya bayyana cewa sulhu da ƴan bindiga ba shi da wani amfani domin tuban muzuru suke yi.

"Dama tun farko gwamna ya ce ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba kuma wannan mataki ne mai kyau. Abin da ya dace da su shi ne a ci gaba da yi musu luguden wuta."

- Jamilu Musa

An caccaki Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya daina ɗora alhakin matsalar rashin tsaro kan Alhaji Bello Matawalle.

Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda ya buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng